logo

HAUSA

Shugaban kasar Angola ya gana da ministan wajen kasar Sin

2023-01-14 14:50:59 CMG Hausa

Shugaba Joao Lourenco na Angola, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, dake ziyarar aiki a birnin Luanda fadar mulkin kasar.

Yayin zantawar su a jiya Jumma’a, shugaban na Angola, ya yabawa ayyukan ginin filin jiragen sama, da cibiyar samar da lantarki ta ruwa, da hanyoyin mota, da tashoshin ruwa, da sauran manyan ayyukan jin dadin al’umma da Sin ta tallafa wajen gudanar da su yadda ya kamata a kasar sa, da ma irin rawar da Sin din ke takawa, wajen sake ginin Angola bayan yaki, da tallafin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.

Shugaba Lourenco, ya ce kasar sa na fatan kara zurfafa hadin gwiwa da Sin, tana kuma maraba da karin sassan Sin, dake da burin zuba jari a kasar.

Shugaban na Angola ya kara da cewa, Sin da Angola, suna da mahanga ta neman samun ci gaba iri daya, kuma Angola na nacewa manufar Sin daya tak a duniya, kuma za ta ci gaba da yin aiki tare da Sin, a fannin kare manufar kaucewa tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, da kare gaskiya da adalci a harkokin kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, Qin Gang cewa ya yi, albarkacin kwazo, da nacewa turbar da shugabannin kasashen biyu suka amincewa, sannu a hankali an kai ga inganta, da zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da kawancen gargajiya tsakanin Sin da Angola. Kaza lika hadin gwiwar su a zahiri, ya haifar da alherai masu tarin yawa.

Qin ya tabo batu, kan yadda a ranar Alhamis, shugabannin kasashen 2 suka taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen su, wanda hakan ya yaukaka alakar dake tsakanin su.

Ministan harkokin wajen na Sin, ya kara da cewa, Sin ta gamsu da yadda Angola ke nacewa manufar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan ta ga shawarwarin kasar Sin, yana mai cewa, har kullum Sin za ta ci gaba da tallafawa Angola ta fuskar nuna adawa da tsoma bakin sassan waje, da baiwa kasar damar zabar turbarta ta ci gaba, da kare ‘yancin yankunan ta, da tsaro da moriyar ci gaban ta.

A daya hannun kuma, a jiya Jumma’a, Qin ya tattauna da takwaransa na Angola Tete Antonio. (Saminu Alhassan)