Xinjiang na tafiya kan tafarki na gari, in ji shugaban majalissar musulmi ta kasa da kasa
2023-01-14 15:14:38 CMG Hausa
Shugaban majalissar musulmi ta kasa da kasa Ali Rashid Al Nuaimi, ya ce saurin ci gaban da jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai ta samu, ya shaida yadda al’amuran jihar ke tafiya bisa turba ta gari.
Daga ranar 8 zuwa 11 ga wata, Ali Rashid Al Nuaimi ya jagoranci tawagar manyan malaman addinin musulunci da kwararru mai kunshe da malamai sama da 30, daga kasashe 14, a ziyarar gani da ido a birnin Urumqi fadar mulkin jihar Xinjiang.
Al Nuaimi, wanda ya kuma ziyarci jihar Xinjiang ta arewa maso yammacin Sin a shekarar 2019, ya yi waiwaye game da tarihin yankin, ta fuskar yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.
Al Nuaimi ya kara da cewa, ‘yan ta’adda ba sa martaba dokokin ko wace kasa, kuma ba sa martaba hakkin bil adama ko ‘yancin al’umma, suna hallaka wadanda ba su ji ba ba su gani ba, kamar yadda suke yin hakan a sauran kasashen duniya.
Ya ce kasar Sin ta yi abun da ya kamata, a fannin aiwatar da dukkanin matakai na kare moriyar ta, da ta al’ummar kasa. Al Nuaimi, ya kara da cewa, Sin ba ta da wata mummunar aniya game da musulmi ko musulumnci, karkashin al’adun ta na gargajiya. Ya kuma jaddada cewa, Sin da akidun Islama suna da dogon tarihi na kasancewa tare, inda suka kasance kawaye dake da hadin gwiwa na kut da kut.
Malamin ya ce duniya na bukatar kasar Sin mai tsaro, da daidaito da walwala, kamar yadda ake bukatar hakan a sauran kasashe masu tasowa.
Bugu da kari, Al Nuaimi ya ce ya sake jagorantar wata tawaga zuwa jihar Xinjiang, domin baiwa al’ummar musulmin duniya damar kara fahimtar Xinjiang. Ya ce akwai bukatar ajiye siyasa a gefe guda, da ma sauran banbance banbancen akidu, a mayar da hankali ga martaba banbance banbancen dake tsakanin sassa daban daban. Ya ce "Dole mu kasance masu karhin fafin gaskiya da babbar murya, kan abun da muka yi imani da shi”. (Saminu Alhassan)