logo

HAUSA

Ya kamata kasar Amurka ta biya karin diyya ga tsibiran Marshall

2023-01-13 10:40:18 CMG Hausa

A kwanan baya wasu kungiyoyin kasa da kasa fiye da 100 sun bukaci gwamnatin kasar Amurka, don ta cika alkawarinta na neman afuwa da biyan isasshiyar diyya ga jamhuriyar tsibiran Marshall, sakamakon gwaje-gwajen nukiliyar da ta gudanar a shekarun 1940 da na 1950.

Wannan batu ya nuna yadda bangarorin kasa da kasa ke neman tabbatar da adalci a duniya, da nuna adawa ga yunkurin kasar Amurka na samun bazuwar makaman nukiliya.

A tsakanin shekarar 1946 da ta 1958, kasar Amurka ta gudanar da gwaje-gwajen fashewar makaman nukiliya a tsibiran Marshall har sau 67, lamarin da ya lalata muhallin tsibiran sosai.

Daga baya, sakamakon matsin lamba daga gamayyar kasa da kasa, kasar Amurka ta yarda da biya jama’ar kasar tsibiran Marshall diyya, yayin da kasashen 2 suka kulla wata yarjejeniya a shekarar 1986. Sai dai daga lokacin har zuwa yanzu, kasar Amurka diyyar dalar Amurka miliyan 4 kawai ta biya.

Kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ya gudanar da wani taro a shekarar 2022, inda ya bukaci kasar Amurka da ta daidaita matsalar da ta haddasa a tsibiran Marshall. Ya kamata kasar Amurka ta saurari kiraye-kirayen da duniya ke yi na neman adalci, ta biya diyyar da ta dace ga kasar tsibiran Marshall, da dakatar da aikinta na neman bazuwar makaman nukiliya a duniya. (Bello Wang)