logo

HAUSA

Ban kwana da Pele: Daga karamin mafari zuwa gagarumar daukaka

2023-01-13 15:45:42 CMG Hausa

Watanni 3 gabanin bikin cikar sa shekaru 10 a duniya, Pele ya yiwa mahaifin sa wato Dondinho alkawari. Sun kammala jin wani shirin radio da aka watsa ke nan game da wasan kwallon kafa tsakanin Brazil da Uruguay, inda Uruguay din ta doke Brazil da ci 2 da nema. An buga wasan na cin kofin duniya ne a shekarar 1950, a filin wasa na Maracana dake birnin Rio de Janeiro. Wasa ne da ya yi matukar kayatarwa, wanda daga baya aka rika yi masa lakabi da “Maracanazo”.

Yayin wata zantawa da FIFA a shekarar 2014, Pele ya ce "A karon farko na ga mahaifi na yana kuka. Na fada masa cewa, ka daina kuka Baba, zan lashe kofin duniya saboda da kai".

A wancan lokaci Dondinho, bai kawo cewa bayan shekaru 8 da wancan alkawari na dan da ya haifa ba, Pele zai cika alkawarin, ta hanyar jagorantar kungiyar Brazil zuwa lashe gasar kwallon kafar ta duniya, a wasan da aka buga a filin wasa na Rasunda dake birnin Stockholm, inda Pele ya kasance dan wasa mafi kankantar shekaru na farko, da ya kai ga lashe kofin duniya na FIFA.

A wannan karo kuwa, mahaifin Pele ya yi kukan murna ne, kasancewar kasar sa Brazil ta yi nasarar lashe kofin duniya, a gabar da duniya ta samu karuwar sabon gwarzon kwallon kafa.

Sunan Pele na ainihi shi ne, Edson Arantes do Nascimento, an kuma haife shi a wani garin manoma da ake kira Tres Coracoes, wanda ke yankin Minas Gerais na kudu maso gabashin kasar Brazil, kuma mahaifin sa Dondinho, ya taba bugawa kulaflikan Fluminense da Celeste Arantes kwallo.

An ce ya samu lakabin Pele ne, saboda gazawar sa ta furta sunan mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Vasco de Gama wato “Bile”, wanda hakan ke baiwa abokan sa mamaki a lokacin.

Ya taso cikin rayuwa ta rashin cikakkiyar wadata, inda ya fara aiki a matsayin sabis, a wani shagon sayar da shayi. Pele ya fara nuna sha’awar buga kwallon kafa tun yana karami, inda ya rika buga kwallo da ya yi ta hanyar cika wata safar kafa da takardu, saboda iyayen sa ba za su iya saya masa kwallon kafa ba.

Cikin kankanen lokaci sai basirar sa ta bayyana, kuma yayin da ya cika shekaru 15, ya kai ga sanya hannu kan kwangilar bugawa babbar kungiyar kwallon kafa ta Brazil wato Santos kwallo. Kuma cikin shekara guda ya zamo ja-gaba cikin ‘yan wasan gaban Santos, har ya kai kungiyar ga zama zakara a karon farko a watan Yulin shekarar 1957, watanni 10 kacal da fara buga gasar ajin kwararru ta kasar, daga nan ne kuma aka kira shi tawagar kasar Brazil, domin shiga kungiyar dake wakiltar kasar a gasannin kasa da kasa.

Pele ya yi fitarsa ta farko a gasar kasa da kasa ne, a wasan da Brazil ta yi rashin nasara hannun Argentina da ci 2 da 1, a filin wasa na Maracana, kuma a wannan wasa ne ya kafa tarihin kasancewa dan wasa mafi karancin shekaru da ya ciwa Brazil kwallo, inda a lokacin yake da shekaru 16 da watanni 9 a duniya.

Yana dan shekara 17 kuma, Pele ya buga gasar cin kofin duniya na shekarar 1958, sai dai a lokacin yana fama da ciwo a gwiwar sa, don haka bai bugawa Brazil wasannin farko guda 2 ba, wato wasannin da ta buga da Austria, da kuma England. Bayan ya samu sauki, sai ya buga wasan karshe na rukuni, inda ya taimakawa Brazil ta doke tarayyar Soviet da ci 2 da nema.

Kaza lika ya ci kwallo daya tak, da ta baiwa Brazil damar lashe wasan ta da Wales, kafin ya ciwa Brazil kwallaye 3 a ragar Faransa, a wasan kusa da na karshe. A wasan karshe ma ya Pele ya taimakawa Brazil doke Sweden da ci 5 da 2, inda a lokacin ne kuma Pele ya tabbatar da matsayin sa, na sabon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya.

Yayin wata zantawa da ‘yan jarida, dan wasan tsakiya na kasar Sweden Sigvard Parling, ya ce "Lokacin da Pele ya ci kwallo ta 5 a wasan karshe da suka doke mu, a gaskiya ni da kai na, sai da ji kamar na tafa masa saboda irin kwarewar da ya nuna".

A shekarar 1962 an buga gasar cin kofin duniya a Chile, a lokacin Pele na da shekaru 21, ana kuma kallon sa a matsayin dan wasan da ya fi ko wanne kwarewa a duniya. A wasan farko da Brazil ta buga ya ci kwallo 1, inda aka tashin Brazil na da kwallo 2 Mexico na da ci 1, amma sai ya yi rauni a wasa na 2 da suka buga da Czechoslovakia, wanda hakan ya hana shi buga ragowar wasannin gasar.

Kasancewar ba ya cikin fili, dan wasan Brazil Mane Garrincha ya maye gurbin sa a matsayin jagoran kungiyar, har ta kai ga daga kofin na gasar kasar Chile, bayan sun doke Czechoslovakia  da ci 3 da 1 a wasan karshe.

Masu sha’awar kwallon kafa sun rasa damar ganin wasa mai burgewa daga Pele, a gasar da ta biyo bayan ta Chile bayan shekaru 4. Domin kuwa a gasar kasar Ingila, lokacin yana da shekaru 25, abokan karawar kungiyar Brazil sun rika yi masa keta a duk lokacin da suka samu damar hakan, domin dakile tasirin sa. Hakan ne kuma ya sanya shi jin rauni a wasan Brazil da Bulgaria, da wanda suka buga da Portugal, har dai ta kai an fitar da Brazil daga gasar tun a zagayen farko.

Daga wannan ne kuma Pele ya sha alwashin ba zai sake buga gasar cin kofin duniya ba, kafin daga bisani ya sauya ra’ayi, ya kuma shiga jerin ‘yan wasan Brazil da suka buga gasar Mexico ta shekarar 1970. Pele ya buga kaso 53 bisa dari na wannan gasa, ya ci kwallaye 4, ya taimaka an ci 6, inda ya kai ga samun kyautar kwallon zinari da ake baiwa dan wasa mafi kwarewa a gasar cin kofin duniya, kana Brazil ta sake lashe kofin na FIFA a wannan shekara.

Pele ya kammala buga wasannin kasa da kasa ne a shekarar 1971, amma ya ci gaba da bugawa kungiyar Santos wasa, inda tare da shi kungiyar ta lashe dukkanin kofunan gasannin da ta buga, har zuwa shekarar 1974, lokacin da ya bayyana yin ritaya daga kwallo baki daya, yana da shekaru 34 a duniya.

Duk da cewa, ya sha kaucewa zuwa turai domin buga wasa a kulaflikan da suka rika gayyatar sa, kasa da shekara guda bayan ya yi ritaya, kungiyar Cosmos ta birnin New York ta lallami Pele, har ya amince ya sake komawa buga kwallo a kungiyar, inda aka yi masa alkwarin makudan kudade.

Pele ya amince ya fara buga kwallo a Cosmos, inda ya ci kwallaye 37 a wasanni 64, ya kuma jagoranci kungiyar dake arewacin Amurka inda ta lashe gasar zakaru ta shekarar 1977.

Pele ya kawo karshen buga kwallo bayan shafe shekaru 21, yana da kwallaye 732 a wasanni 792 da ya bugawa kasar sa, da kuma kulaflikan da ya bugawa wasa.

Wannan wani tarihi ne mai ban sha’awa da ya kafa a tarhin kwallo, a matsayin sa na mai taimakawa ‘yan wasa masu kai hari, sabanin dan wasan gaba mai cin kwallo. 

Tun da ya kafa tarihin yawan cin kwallaye 77 a wasannin kasa da kasa 92, ba a samu wani dan wasa da ya kai ga hakan ba, sai a watan Disambar da ya gabata, da dan wasan Brazil Neymar, shi ma ya kafa irin wannan tarihi, a wasan kuda da kusan na karshe da Brazil ta buga a Qatar.

Pele ne dan wasa daya tilo da ya lashe gasar cin kofin duniya na FIFA sau 3, kuma a shekara ta 2000, aka rabawa Pele da Diego Maradona na Argentina kyautar kasancewa ‘yan kwallon kafar wannan karni. 

A kuma wannan shekara ne, kwamitin shirya gasar wasannin  Olympic ta kasa da kasa, ya zabi Pele a matsayin dan wasan motsa jiki na karni, kana mujallar “Time” ta sanya shi cikin jerin mutane 10 mafiya shahara a duniya, na shekarun 1900.