logo

HAUSA

A karo na farko kudin cinikin waje na kasar Sin ya zarce Yuan tiriliyan 40

2023-01-13 21:47:16 CMG Hausa

A karo na farko, kudin cinikin waje na kasar Sin ya zarce kudin kasar Yuan tiriliyan 40, kana Sin ta zama babbar kasar cinikin hajoji ta farko a duniya cikin shekaru shida a jere! Sakamakon cinikin waje na kasar Sin na shekara ta 2022 da aka fitar a yau Jumma’a 13 ga wata, ya kara karfafa imanin kasa da kasa kan tattalin arzikin kasar ta Sin.

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da alkaluman dake bayyana cewa, darajar cinikin shige da ficen kayayyaki da kasar Sin ta yi a shekara ta 2022, ta zarce kudin kasar Yuan tiriliyan 42, wanda ya karu da kaso 7.7 bisa dari na shekara ta 2021.

Duba da yadda duniya take fuskantar matsalolin tawayar tattalin arziki, da yaduwar annobar COVID-19, ba abu ne mai sauki kasar Sin ta cimma wannan nasara a fannin cinikin waje ba. Kuma hakan na nuna cewa, tattalin arzikin kasar na da makoma mai haske, kuma zai bunkasa yadda ya kamata a cikin dogon lokaci.

A wajen taron da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya shirya kan harkokin tattalin arziki a karshen shekarar bara, fadada bukatun cikin gida, da kara bude kofa ga kasashen waje, muhimman abubuwa ne da aka tattauna. Hakan na nuna cewa, a bana, cinikin waje na kasar Sin zai kara bunkasa, wanda zai taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasar, don bayar da muhimmiyar gudummawa ga habakar tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)