logo

HAUSA

Shugaban Gabon ya gana da ministan wajen Sin kan karfafa alaka tsakanin kasashen biyu

2023-01-13 09:54:58 CMG HAUSA

 

A jiya ne, shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang a birnin Libreville, babban birnin kasar. A yayin ganawar tasu, Qin ya isar da sakon gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaban Gabon, inda ya bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Gabon, wadda tsoffin shugabannin kasashen biyu suka kulla tare, ta jure wahalhalu, kuma ta ci gaba da inganta.

Qin ya kara da cewa, Sin da Gabon suna goyon bayan juna sosai kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyarsu, da manyan batutuwa dake shafar kasashen biyu, da kiyaye muhimman ka'idoji da suka shafi huldar kasa da kasa, da tabbatar da adalci da daidaito a duniya. A nasa bangare kuwa, shugaban kasar Gabon, ya bukaci Qin da ya mika sakon gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping, inda ya mika godiyarsa ga kasar Sin bisa cikakken goyon baya da take baiwa kasarsa, wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

A cewarsa, dangantakar kasashen biyu ta kara karfi yayin da kasashen ke inganta ci gaba tare da kiyaye moriyarsu. (Ibrahim Yaya)