Sin ta bukaci Amurka da ta kalli dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da idon basira
2023-01-12 10:04:28 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, kasarsa ta bukaci Amurka, da ta kalli dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka bisa gaskiya da idon basira.
Wang Wenbin ya bayyana hakan ne, jiya Laraba yayin wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka bukaci ya yi karin haske, game da wani kwamiti da majalisar wakilan Amurka ta kafa a kan kasar Sin.(Ibrahim)