logo

HAUSA

Ma`aikatar lafiya a tarayyar Najeriya ta musanta zargin odar magunguna jabu

2023-01-12 10:03:13 CMG HAUSA

 

A ranar 11 ga wata yayin wani taron manema labarai, ministan lafiya a tarayyar Najeriya Dr. Osagie Ehanire ya ce ba gaskiya ba ne zargin da ake cewa magungunan da ake samarwa a kasar karkashin shirin inshorar lafiya ba su da inganci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi bagwai ya halarci taron manema labaran da aka gudanar a ma’aikatar yada labarai da al’aldu.//////

 

Taron manema labaran ci gaba ne daga cikin jerin bayanai game da nasarorin da gwamantin tarayyar Najeriyar ta samu a kan sha’anin kiwon lafiya tun daga shekarar 2015 zuwa watan Janairun 2023.

Bayan tambayar da wani daga cikin manema labarai ya yi wa ministan kan cewa magungunan da ake baiwa marasa lafiya dake cin gajiyar shirin inshorar lafiya a tarayyar Najeriya suna da sauki matuka, amma kuma ingancinsu ya bambanta da na sauran marasa lafiyar da ba sa cikin shirin.

Dr Osagie Ehanire ya ce akasarin magungunan da ake bayarwa karkashin shirin inshorar lafiyar ba sa dauke da tambarin kowanne kamfani wannan shi ne ya sanya suke da saukin gaske, amma fa aiki daya suke yi da na sauran magunguna.

Da yake karin haske kan batun, babban sakatare a hukumar inshorar lafiya ta kasa a tarayyar Najeriya Farfesa Mohammed Sambo ya ce, yanzu haka dai shirye-shirye sun yi nisa wajen rarraba magunguna da suke dauke da shedar hukumar ga asibitocin kasar domin a rinka baiwa marasa lafiyar da suka yi rijista da shirin.

“Kamfanonin samar da magunguna a Najeriya dukkanninsu sun amince bayan da minista ya sahale masu su rinka sanya alamar hukumar ta NHIS a jikin magungunan da suke samarwa, kuma gwamnati za ta saya sannan ta rarraba su ga asibitocin ta don a baiwa marasa lafiyar da ake kula da su karkashin shirin.

“Ka ga ke nan babu wani kuma da zai sake korafin cewa magungunan da ake bayarwa na jabu ne ko kuma ba su da inganci , kuma nan da ’yan makonni wannan tsarin zai kankama.”

An dai fara aiwatar da shirin inshorar lafiya a tarayyar Najeriya a shekarar 2005 da nufin samar da sauki ga ’yan kasa wajen kula da lafiyar su ta hanyar samar masu da magunguna kan farashi mai sauki inda za su rinka biyan wani kaso daga cikin farashin da gwamnati ta kayyade.

To sai dai kuma har yanzu shirin bai kai ga nasarar da ake bukata ba idan aka yi la’akari da yawan mutanen da suke cin gajiyar shirin musamman ma a yankunan karkara. (Garba Abdullahi Bagwai)