Ministan harkokin wajen Sin ya gabatar da shawarwarin raya huldar Sin da Afrika
2023-01-12 10:46:23 CMG HAUSA
Ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya ce, a shirye Sin take ta hada hannu da kasashen Afrika, wajen zurfafa dangantakar abota tsakaninta da kasashen Afrika da daukaka hadin gwiwarsu a sabon zamani.
Qin Gang, wanda ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai tare da shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, a Addis Ababa na kasar Habasha, inda hedkwatar AU take, ya gabatar da wasu shawarwari 4 dangane da raya huldar Sin da Afrika.
Da farko, ya jadadda bukatar gaggauta musaya ta zahiri game da burikan da ake son cimmawa, tsakanin bangarorin biyu.
Na biyu, ya yi kira da a zurfafa kawance tsakanin Sin da Tarayyar Afrika AU.
Na uku, ya ce ya kamata a yi kokarin daukaka hadin gwiwar Sin da Afrika, da gaggauta aiwatar da sakamakon taro na 8 na ministoci, karkashin dandalin FOCAC.
Na hudu, ministan na Sin ya ce akwai bukatar karfafa goyon bayan juna da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa.
Yayin da yake halartar bikin murnar kammala ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC, a karkarar kudancin birnin Addis Ababa, Qin Gang ya ce kasar Sin za ta bayar da gagarumar gudunmawa ga bangaren kiwon lafiya da na rayuwar al’’ummar nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)