logo

HAUSA

Kasar Sin za ta bayar da rance mai rangwame ga aikin samar da sadarwar intanet a Angola

2023-01-12 11:34:34 CMG HAUSA

 

Kasar Sin za ta samar da rancen kudi domin taimakawa shirin samar da tsarin sadarwar intanet na kasar Angola, karkashin yarjejeniyar rance mai rangawame da aka rattabawa hannu jiya Laraba.

Karkashin yarjejeniyar, bankin kula da harkokin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin, zai samar da kudin da ya kai dala biliyan 249, domin shimfida hanyar sadarwar intanet mai tsawon kilomita 2,000 da za ta bi karkashin kasa da kuma wadda za ta hada kasar da yankin Cabinda da ruwa ya ratsa tsakaninsu, tare kuma da inganta baki dayan tsarin sadarwar kasar. (Fa’iza Mustaph)