logo

HAUSA

Sojojin Sudan ta Kudu sun fatattaki ‘yan bindiga a Upper Nile da Pibor

2023-01-12 09:16:49 CMG Hausa

Dakarun tsaron Sudan ta Kudu (SSPDF) sun bayyana cewa, sun yi nasarar fatattakar mayakan sa kai na White Army a jihar Upper Nile da kuma yankin Greater Pibor (GPAA).

Mai magana da yawun SSPDF Lul Ruai Koang, ya shaidawa manema labarai a Juba, babban birnin kasar cewa, an samu kwanciyar hankali a Upper Nile da GPAA, tun bayan da suka fatattaki mayakan sa kan, wadanda galibinsu mayakan Lou-Nuer ne daga jihar Jonglei.

Koang ya ce, dakarun tsaron kasar sun kuma fatattaki mayakan Lou-Nuer a Greater Pibor. A watan Nuwamban shekarar 2022 ne, mayakan White Army suka kai hari a gundumar Fashoda na jihar Upper Nile, inda suka raba fararen hula sama da 30,000 da muhallansu. A ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, shugaba Salva Kiir ya ba da umarnin da a dawo da sarkin Chollo zuwa birnin Juba, bayan barazanar da aka yi wa rayuwarsa.(Ibrahim)