Sin ta jinjinawa matakin PNG na rufe ofishin cinikayyar yankin Taiwan dake kasar
2023-01-12 19:42:19 CMG Hausa
Kasar Sin ta jinjinawa matakin gwamnatin kasar Papua New Guinea ko PNG, na rufe ofishin cinikayyar yankin Taiwan dake kasar. Da yake amsa wata tambaya mai alaka da batun a yau Alhamis, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta yi matukar amincewa da wannan mataki.
Wang ya kara da cewa, matakin da mahukuntan PNGn suka dauka, ya sake tabbatar da matukar karbuwar manufar nan ta “kasar Sin daya tak a duniya” a tsakanin sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)