logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Angola sun taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu

2023-01-12 14:08:23 CMG HAUSA

 

Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wa takwaransa na kasar Angola João Manuel Gonçalves Lourenço sakon taya juna murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu.

Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, kasashen biyu na nacewa ga sahihin zumunci tare da samun ci gaba cikin hadin kai, kazalika suna amincewa da goyon bayan juna kan muradunsu da manyan abubuwan dake jan hankalinsu.

A nasa bangare Lourenço ya ce, tun kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, ana ci gaba da samun bunkasuwar huldarsu, kana sun samu ci gaba mai armashi cikin hadin kai a bangarori daban-daban, sakamakon dake gamsar da bangarorin biyu. (Amina Xu)