logo

HAUSA

Najeriya na shirin samar da karin iskar shaka ga marasa lafiya dake mutukar bukata

2023-01-11 09:17:17 CMG Hausa

A ranar Talata 10 ga wata, ma’aikatar lafiya a tarayyar Najeriya ta ce gwamnati na shirin samar da karin masana’antun samar da iskar shaka ga marasa lafiya dake mutukar bukata.

Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin taro karo na 17 wanda ake tabo nasarorin gwamnati a fagen sha’anin kiwon lafiya.

Dr. Osagie Ehanire ya ce kafin bullar annobar COVID-19 a shekara ta 2020, Najeriya na da masana’antun sarrafa iska guda 30 ne kawai, amma bayan bullar annobar gwamnati ta matsa kaimi wajen samar da karin masana’antun.

Ministan ha’ila yau ya ce annobar COVID-19 ya sanya gwamnati ta kara farkawa wajen samar da dakunan gwaje-gwajen kwayoyi cutar da suke da nasaba da numfashi a dukkannin cibiyoyin lafiya mallakin gwamnatin tarayya dake jahohi.

Ministan lafiyar na tarayyar Najeriya ya kara da cewa gwamnati ta samu cimma nasarar samar da karin masana’antun sarrafa iskar shaka ga marasa lafiya bisa irin gudummawar da ta samu daga manyan cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da kuma hukumar UNICEF, wanda yanzu haka akwai irin wadannan masana’antu sama da 100 da suke aiki. (Garba Abdullahi Bagwai)