Sin: Ziyarar Qin Gang a Afirka bayan da ya kama aiki na da nufin zurfafa zumuncin gargajiya
2023-01-11 20:38:21 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya fara a wasu kasashen Afirka, jim kadan da kama aikin sa, ta shaida yadda kasar Sin ke darajanta zumuncin da ke tsakaninta da kasashen Afirka, wadda kuma ke da nufin kara dinke zumuncin sassan biyu.
Wang Wenbin, ya ce bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan harkokin wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara kasashen Afirka.
A ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata ne aka nada Qin Gang a matsayin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya kuma fara ziyarar a ranar Talata, inda ya fara da yada zango a kasar Habasha. (Saminu Alhassan)