logo

HAUSA

Sin ta dage damar biza kyauta ga ‘yan kasashen Koriya ta kudu da Japan dake yada zango a kasar

2023-01-11 20:29:14 CMG Hausa

A Larabar nan ne gwamanatin kasar Sin, ta dage damar da ‘yan kasashen koriya ta kudu da Japan ke samu a baya, ta samun Biza daga tashoshin shigowa kasar Sin, da kuma Biza kyauta ta sa’o’i 72/144, ga fasinjojin kasashen 2 dake yada-zango a kasar Sin a kan hanyar su ta zuwa sauran kasashen duniya.

Wannan mataki dai na zuwa ne, bayan da wasu tsirarrun kasashen duniya suka sanya wasu sharuddan nuna bambanci ga Sinawa masu shiga kasashen, kamar dai yadda hukumar lura da shige da fice ta kasar Sin ta bayyana. (Saminu Alhassan)