Duniya ta fara amfana da sabbin matakan Sin na kandagarkin COVID-19
2023-01-11 10:03:19 CMG Hausa
A kwanakin baya ne mahukuntan kasar Sin, suka sanar da kyautata matakan kasar na yaki annobar COVIUD-19, wanda ya fara aiki tun daga ranar 8 ga watan Junairu, inda karkashinsa, aka soke gwajin cutar COVID-19 ga matafiya daga ketare da za su shiga kasar.
Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ana shawartar masu zuwa kasar Sin daga ketare, su yi gwajin cutar sa’o’i 48 kafin lokacin tafiyarsu. Inda kuma ake shawartar wadanda gwaji ya nuna sun kamu da cutar, su jinkirta tafiyar zuwa lokacin da gwaji zai nuna ba sa dauke da ita.
Haka kuma, babu bukatar matafiya su nemi manhajar tantance yanayin cutar ta Health Code, daga ofisoshin jakadancin kasar Sin, kafin shiga kasar. Abin da ake bukata yanzu shi ne, matafiya za su bayyana yanayin lafiyarsu ne a katin da za su gabatarwa jami’an kwastam. Wadanda kuma yanayin lafiyarsu ke da matsala ko suke dauke da zazzabi, za su yi gwaji a wurin, sannan kuma za a nemi su killace kansu a gida ko su je asibiti, bisa la’akari da yanayin lafiyarsu.
Wasu daga cikin dalilan da kasar Sin ta dauki wadannan matakai, sh ne raguwar karfin illar da kwayoyin cutar COVID-19 ke haifarwa, kana fiye da kashi 90 cikin 100 na al’ummar kasar, sun karbi cikakkun alluran rigakafin cutar, yayin da kasar ita ma ta samu ci gaba sosai a fannin kirkiro magunguna da adana isashen kayayyakin da ake bukata don jinyar mutanen da suka kamu da cutar COVID, suka sa kasar Sin samun damar daidaita manufarta ta dakile annoba, tare da saukaka matakan shigi da fici.
Tun bayan fara aiwatar da wannan manufa, harkokin zirga-zirgar jiragen saman kasa da kasa da cinikayya da yawon shakatawa da makamantansu suka fara kankama, ba ma kasar Sin ba, har a sassan duniya. Wannan a cewar masana zai taimaka matuka wajen farfado da tattalin arzikin duniya da ya fuskanci koma baya sakamakon annobar da ta addabi duniya cikin shekaru kusan uku da suka gabata. Sai dai yayin da wasu kasashen yamma ke neman siyasantar da matakin na kasar Sin, wasu kasashe kuma na murna har ma sun fara tallata wurarensu na yawon shakatawa tare da marabtar Sinawa masu bukatar zuwa yawon bude ido kasashen nasu. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)