logo

HAUSA

Amurka ta fi kawo cikas ga aikin yaki da cutar COVID-19 a duniya

2023-01-11 12:12:19 CMG Hausa

Kasar Amurka ta maida kanta matsayin kasa mafi samar da kyautar alluran rigakafin cutar COVID-19 a duniya, inda ta yi alkawarin samar da alluran rigakafin a kalla biliyan 1 da miliyan 100 ga duk duniya kafin shekarar 2023, amma ya zuwa ranar 5 ga wannan wata, allurai miliyan 665.1 kawai ta samar. Kana Amurka ta kai alluran da suka kusa lalacewa zuwa kasashen Afirka, don cika alkawarinta na samarwa kasashen Afirka alluran kyauta, sai dai kasashen Afirka ba su ji dadin hakan ba. 

Bisa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, an ce, kasashen da kasar ta fi samarwa alluran rigakafin cutar kyauta su ne wadanda ke kewayen kasar Sin. Bisa nazarin da aka yi, an ce, gwamnatin Amurka tana son yin amfani da alluran don tilasta wa kasashen dake kewayen kasar Sin su shiga kawancen kin kasar Sin, batun da ya kawo illa ga yanayin hadin gwiwar yaki da cutar a duniya.

Haka zakila, yayin da ake tinkarar matsalar karuwar mutuwar mutane a sakamakon mummunar cutar, Amurka ta kore bakin haure masu dimbin yawa, hakan ya kara yaduwar cutar a kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Latin Amurka.

Kasar Sin kuwa ta tabbatar da kiyaye lafiyar jama’arta fiye da biliyan 1 da miliyan 400 a cikin shekaru 3 da suka wuce, kana ta hada gwiwa da kasa da kasa wajen yaki da cutar ta COVID-19. A cikin shekaru 3 da suka wuce, kasar Sin ta yi musayar fasahohi fiye da 60 tare da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO. Ya zuwa yanzu kuma, kasar Sin ta samar da kayayyakin yaki da cutar fiye da daruruwan biliyoyi ga kasashe 153 da kungiyoyin kasa da kasa 15, kana ta samar da alluran rigakafin cutar fiye da biliyan 2.2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120.

Ana iya gano wanda ya samar da gudummawa ga duniya wajen yaki da cutar, da wanda ya kawo cikas ga aikin. Amurka ta fi kawo cikas ga aikin yaki da cutar a duniya. (Zainab)