logo

HAUSA

Firaministan Habasha ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang

2023-01-11 12:10:21 CMG Hausa

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang dake ziyara a kasar a birnin Addis Ababa.

Firaminista Abiy ya bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin ya zabi kasar Habasha a matsayin zango na farko na ziyararsa bayan hawan kujerar mukaminsa, lamarin da ya shaida zumunta mai zurfi da muhimmancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce an samu nasarori da dama kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Habasha da kasar Sin a fannonin ayyukan more rayuwa, da tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da aikin gona, da gina yankin raya masana’antu da dai sauransu, wadanda ke da babbar ma’ana, wajen sa kaimi ga raya tattalin arzikin kasar Habasha da sanya ta cikin jerin kasashen dake kan gaba a nahiyar Afirka, kana ya yi maraba da karin kamfanonin Sin da su je kasar Habasha don zuba jari da gudanar da ayyuka.

A nasa bangare, Qin Gang ya bayyana cewa, a cikin fiye da rabin karni bayan kasashen Sin da Habasha sun kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu, ko da yake yanayin duniya ya sauya, kasashen biyu sun ci gaba da goyon bayan juna da yin kokari tare, wanda ya zama misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Ya ce kasar Sin ta nuna goyon baya ga kasar Habasha wajen bin hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayinta. Haka kuma, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, da sa kaimi ga karin kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Habasha da shiga aikin sake gina kasar. Qin ya kara da cewa, kasar Sin tana son kasar Habasha ta samar da yanayi mai kyau na yin ciniki da daukar matakai don tabbatar da tsaro da moriyar ma’aikata da hukumomin kasar Sin. (Zainab)