logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani kan makomar zaman lafiya da ci gaban kahon Afirka

2023-01-11 13:25:00 CMG Hausa

 

Ministan harkokin wajen Sin Qin Gang ya tattauna da manema labarai, tare da mataimakin firaministan Habasha da ministan harkokin wajen kasar Demeke Mekonnen, bayan tattaunawarsu a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Da aka nemi jin ra’ayinsa game da yarjejeniyar zaman lafiya ta Habasha da ci gaban da aka samu dangane da shawarar da Sin ta gabatar ta “Makomar Zaman Lafiya da Ci Gaban Kahon Afrika” a Habasha, Qin Gang ya ce, Habasha gida ne na bai daya ga al’ummar kasar, ciki har da mutanen Tigray.

Ya ce kasar Sin ta kasance mai girmama cikakken ikon Habasha da yankunanta, kana tana mara baya ga gwamnatin kasar da al’ummarta, a kokarinsu na cimma zaman lafiya da hadin kai da kuma neman ci gaba.

Da ya yi waiwaye kan ziyarar manzon musamman na Sin a kahon Afrika, Xue Bing ya kai wasu kasashen yankin, Qin Gang ya ce kasar Sin ta goyi bayan babban taron zaman lafiya na kahon Afrika na farko, wanda ya bayar da gudunmawa ga cimma matsaya tsakanin dukkan bangarori da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin.

Ya kuma bayyana cewa, Sin ta samar da kashi-kashi na kayayyakin abinci da alluran rigakafi da sauran kayayyakin jin kai ga Habasha, domin taimakawa inganta rayuwar al’ummomin dake yankuna masu fama da rikici. (Fa’iza Mustapha)