logo

HAUSA

Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA

2023-01-10 16:15:07 CMG HAUSA



Ronaldo Ya Koma Al-Nassr Ta Saudiyya

Dan wasa Cristiano Ronaldo ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudiyya kamar yadda rahotanni daga kasar suka bayyana.

Ronaldo Mai shekara 37 a duniya yabar Manchester United a cikin watan daya gabata bayan wata hira da yayi da manema labarai inda ya soki kociyan kungiyar da masu kungiyar.


Ana saran Ronaldo dan Portugal zai karbi albashi mai tsoka a Sabuwar kungiyar tasa.

Ana saran a farkon wata mai kamawa na Janairu zai fara bugawa kungiyar tasa wasa.

Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta fuskanci koma-baya a jadawalin kasashe mafi kwarewa a fagen kwallon kafa a duniya kamar yadda hukumar FIFA ta fitar da jadawalin a wannan mako.

 Kafin fitowar sabon jadawalin, Nijeriya na matsayi na 32 a teburin FIFA, sai dai kuma a yanzu ta koma na 35, sakamakon rashin zuwa gasar cin kofin duniya da kuma rashin nasara a wasannin sada zumunta.

Kasar Maroko wadda ta yi rawar gani a gasar kofin duniya da aka kammala ba da jimawa ba a Katar, ta koma na 11 a duniya, sannan ta sauko da Senegal daga ta daya a teburin FIFA na mafi kwarewa a Afrika.

 Kafin a fitar da sabon jadawalin, Maroko na zaune ne ta 22 a duniya, yanzu kuma ta dawo ta 11 bayan da ta kafa tarihin zuwa zagayen kusa da karshe na gasar kofin duniya, wani abu da wata kasa a Afrika ko ta Larabawa ba ta taba yi ba.

Tawagar Super Eagles ta fuskanci koma-baya ne tun bayan gaza doke Ghana a wasan share fage na zuwa gasar kofin duniya, kuma hakan ya hana ta zuwa gasar ta Katar 2022 da aka kammala.

Kawo yanzu dai Brazil ce ke ci gaba da zama ta daya a teburin, Argentina da ta lashe kofin duniya ke bin ta, sai kuma kasar Faransa wadda aka doke a wasan karshe na cin kofin duniya take ta uku.

 

Dan Wasan Duniya, Pele, Ya Rasu Yana Da Shekaru 82

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Pele ya rasu yana da shekara 82.

Pele, dan Brazil ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana Pele ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda

Masu sharhi akan harkokin kwallon kafa suna ganin Pele ne dan kwallon da ba a tana samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya inda ya lashe a shekarun

1958 da 1962 da kuma 1970

Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga kwallo ciki har da kwallo 77 da ya ci wa kasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil.

 

Qatar 2022: Za A Mayar Da Dakin Otal Din Da Messi Ya Zauna Wajen Tarihi

An fara shirye-shiryen mayar da dakin otal din da Lionel Messi, ya zauna lokacin da aka yi Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar wajen tarihi.

Messi dai ya jagoranci Argentina wajen lashe kofin duniya, bayan da ta lashe gasar 1986, bayan doke Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Bolanle Raheem: Sufeton ‘Yansanda Ya Bayar Da Umarnin Dakatar Da ASP Drambi Vandi

Babu Hannunmu Wajen Murdewa Kowa Zabe – INEC

Messi mai shekaru 35 ya lashe gasar a karon farko a tarihin rayuwarsa.

Dan wasan dai a iya cewa ya zama gagara badau, inda ya lashe kusan kowace gasa da ya taba bugawa a rayuwarsa.

Dakin dai za a mayar da shi wajen tarihi idan magoya baya za su koma kallon wajen da zakaran na duniya ya dinga kwana.

Argentina dai ra fara gasar ne da rashin nasara da ci 2-1 a hannun Kasar Saudiyya.

Sai dai tun daga wannan rashin nasara ba ta sake rashin nasara ba har zuwa lokacin da ta lashe gasar.

 

Abinda Ya Hana Messi Dawowa PSG

Kocin PSG Christophe Galtier ya bayyana ainihin lokacin da Lionel Messi zai koma taka leda a tawagarsa.

Messi ya ci gaba da zama a Argentina bayan nasarar da suka samu a kofin FIFA na gasar cin kofin duniya a Qatar, don haka messi ba zai dawo ba sai bayan PSG ta kara da kungiyar Lens a farkon 2023 na gasar Ligue 1.

Lingard Ya Caccaki Man U Kan Yi Masa Alkawuran Karya

Messi ya lashe kofin duniya a kasarsa Argentina, inda ya doke abokin wasansa Kylian Mbappe na Faransa da ci 4-2 a bugun fanareti a wasan karshe.

Mbappe ya dawo atisaye a Faransa amma Messi yana can yana murnar nasarar da ya samu a kasarsa.


Tun Da Mu Ka Yi Sakaci Liverpool Ta Saye Gakpo, Dole Mu Sa Yi Ramos

Kocin Manchester United Erik ten Hag yana son kungiyarsa ta sai masa dan wasan gaban Benefica, Goncalo Ramos bayan Liverpool ta doke su a takarar siyan Cody Gakpo.

United ta yi kokarin dauko Gakpo daga PSV a lokacin bazara amma a maimakon haka ta zabi kammala cinikin Antony kan fan miliyan 85.

Lingard Ya Caccaki Man U Kan Yi Masa Alkawuran Karya

Ana sa ran kungiyar Manchester za ta koma sayen dan wasan mai shekara 23, amma Liverpool ta shiga yarjejeniya da kulob din na Holland kan fan miliyan 50.

A cewar jaridar The Mirror, Ten Hag yanzu yana burin dauko Ramos.

Ramos shi ne wanda ya zura kwallaye uku a ragar Switzerland a karawar kasarsa (Portugal) a zagayen 16 na karshe a gasar cin kofin duniya a farkon watan nan, darajar dan wasan ta kai yuro miliyan 120 (£103m) a kwantiraginsa.

Dan wasan mai shekaru 21 ya kuma zura kwallaye tara a gasar ya zuwa yanzu.