logo

HAUSA

An kara cimma nasarori a fannin hadin-gwiwar Sin da Afirka a shekara ta 2022

2023-01-10 14:44:50 CMG Hausa

A shekarar da ta shude wato 2022, duniya ta fuskanci wasu manyan sauye-sauye da kalubaloli da dama, ciki har da yaduwar annobar numfashi ta COVID-19, da matsalar sauyin yanayi, da rikicin kasa da kasa da sauransu. Nahiyar Afirka ta shawo kan kalubaloli daban-daban, ciki har da sauyin yanayi, da tashe-tashen hankali, da rashin isasshen abinci da matsalar jin kai da makamantansu. A bangaren hadin-gwiwar kasashen Afirka da kasar Sin kuwa, an kara cimma nasarori daban-daban, al’amarin da ya sanya sabon kuzari ga shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a nahiyar Afirka.

Inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, daya ne daga cikin fannonin hadin-gwiwar Sin da Afirka. Idan mun dauki Najeriya a matsayin misali, kwanan baya kamfanin gine-gine na kasar Sin CCECC, ya kammala kashi na farko na layin dogo mai amfani da wutar lantarki, a jihar Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya. Duk da cewa kashi na farko na layin dogo na da tsawon kilomita 13 kawai, amma zai taimaka wajen saukaka zirga-zirga ga mazauna Lagos sosai, birni mai cunkoson al’umma sama da miliyan 20. Gwamnatin Lagos ta yiwa aikin lakabi da “Lagos Rail Mass Transit” ko (LRMT) a takaice, kuma a cewar gwamnan jihar Lagos, Babajide Olusola Sanwo-Olu, aikin wani muhimmin al’amari ne mai cike da tarihi.

Daga Najeriya sai mu je Madagascar, inda a arewacin kasar, akwai wata babbar hanya mai suna 5A, wadda ta hada gabar yammaci da gabashi, amma ta kusan lalacewa saboda rashin gyara na dogon lokaci. A lokacin rani, a kan shafe akalla awa 12 kafin a wuce ta hanyar, sai dai a kan shafe makwanni biyu ko fiye a lokacin damina. Bayan da kamfann kasar Sin ya kammala aikin sake gyaran hanyar a cikin kasa da shekaru 3, a halin yanzu awa 2.5 kacal ake dauka don wuce hanyar.

Inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a fannin sufuri, daya ne daga cikin muhimman abubuwa masu taimakawa ci gaban kasashen Afirka. Idan an kyautata harkokin sufuri, za’a kara mu’amala tsakanin yankunan karkara da birane, tsakanin birane da sauran kasashen duniya, ta yadda za’a kara yin jigilar hajoji, kuma tattalin arziki zai bunkasa yadda ya kamata. Tun da aka kafa dandalin tattauna hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC a shekara ta 2000, ya zuwa yanzu, kasar Sin da kasashen Afirka sun hada kai don gina layukan dogo da tsawon su ya zarce kilomita dubu 10, da hanyoyin mota kimanin kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu 1, wadanda suka samar da alfanu ga ci gaban rayuwar mazauna wurin.

Ban da ayyukan sufuri, ayyukan samar da tsaftaccen ruwa da wutar lantarki a kasashen Afirka su ma suna taimakawa sosai ga rayuwar dan Adam.

Alal misali, a jihar Lusaka dake kasar Zambiya, matsalar karancin ruwa ta dade tana ci wa al’ummar wajen tuwo a kwarya. Lokacin da aka dauke ruwan, babu ruwan wanke tufafi, da wanka, har ma da wanda za a tsabtace ban daki. Domin daidaita wannan matsala, kamfanin kasar Sin ya yi amfani da fasahohin kasar a cikin babban aikin samar da ruwa kan kogin Kafue dake Zambiya, wanda ke kunshe da tsare-tsaren debo ruwa, da tsaftace shi, da jigilarsa da sauransu. Irin wannan aikin, zai iya samar da tsaftaccen ruwa da yawansa ya kai cubic mita dubu 50 ga mazauna wurin a kowace rana.

Sai kuma a kasar Burundi dake gabashin nahiyar Afirka, inda kusan babu sabuwar tashar samar da wutar lantarki ko daya dake aiki a cikin shekaru 30 da suka gabata, kana, karancin wutar lantarki ya kawo babban cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Sai dai kamfanin kasar Sin ya gama aikin gina babbar tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Ruzibazi, wadda ke samar da isasshiyar wutar lantarki ga baki dayan birnin Bujumbura, fadar mulkin Burundi a halin yanzu. A nasa bangaren, shugaba Evariste Ndayishimiye na kasar ya ce, ya sha kai ziyara kasar Sin don koyon dabarun ci gaban ta, inda ya fahimci cewa, al’ummar kasar Sin sun samu ci gaban rayuwa saboda jajircewar su a fannin aiki, a don haka, ya yi kira ga al’ummar kasar Burundi, da su koyi yadda mutanen kasar Sin ke nuna kwazo wajen aiki, da kara bayar da gudummawa ga bunkasar tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar Burundi.

Aikin noma, shi ne muhimmin fanni na daban na hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Mu dauki kasar Kenya a matsayin misali, inda masara ta zama daya daga cikin muhimman amfanin gonar kasar, amma yawan masarar da ake nomawa a kasar, bai iya biyan bukatun al’ummar ta ba, musamman saboda bala’in fari mai tsanani, kasashen Afirka da dama, ciki har da Kenya, suna fuskantar rashin ruwa, al’amarin da ya rage yawan amfanin gona da suke samu. Domin warware matsalar, cibiyar nazari ta hadin-gwiwar Sin da Afirka dake Kenya ta yi amfani da fasahohin kasar Sin don fara noman farar masara ta wurin a watan Afrilun bara, har ma yawan masarar da suka girba ya karu da kaso 50 bida dari, wato ya kai kilogiram 2700 a kowace eka. A nasa bangaren, babban darektan cibiyar nazari ta hadin-gwiwar Sin da Afirka a bangaren Afirka, Robert Gituru ya ce, fasahohin kasar Sin a fannin noma na da saukin fahimta da aiki, kuma sun dace da yanayin da manoman Kenya ke ciki. A nan gaba kuma, cibiyar sa za ta wallafa wasu kananan littattafai kan dabarun kasar Sin a fannin noma, don raba su ga manoman wurin, ta yadda za’a kara fadakar da su kan fasahohin kasar Sin.

Samar da isasshen abinci, muhimmin bangare ne a cikin ayyukan hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Ban da tallata fasahohi gami da ire-iren amfanin gonar kasar Sin a Afirka, kasar Sin tana kuma kokarin taimakawa kasashen Afirka kafa masana’antar sarrafa amfanin gona, da horas da kwararrun aikin gona. Alal misali, kasar Sin ta mika masana’antar sarrafa garin masara da ta gina ga gwamnatin kasar Zambiya a watan Yunin shekara ta 2022, kuma a watan Mayun bara, kasar Sin ta shirya kwas din horaswa ga manoman Jamhuriyar Benin game da na’urorin noman auduga, kuma irin wadannan abubuwa ba sa misaltuwa.

Sai kuma a bangaren kasuwanci, akwai hadin-gwiwa mai inganci tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Tun daga watan Afrilu zuwa Mayun shekarar da ta gabata ne, aka gudanar da bikin sayar da hajojin Afirka masu inganci ta yanar gizo a kasar Sin, inda jakadan kasar Rwanda dake kasar, Mista James Kimonyo ya tallata wasu hajojin kasar sa ga masu amfani da Intanet na kasar Sin, inda aka sayar da dukkan kofin da ya zo da su.

A watan Nuwambar shekarar da ta gabata, bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko kuma CIIE da aka gudanar a birnin Shanghai, ya jawo kyawawan hajojin Afirka da yawa, ciki har da kofi daga Habasha, da barkono daga Rwanda, da zuma daga Zambiya, da wasu kayan marmari daga Kenya, wadanda suka samu karbuwa sosai a kasar Sin. Bikin CIIE na bara, ya samu halartar kamfanoni sama da 100 na kasashen Afirka fiye da 30, kuma hajojin da suka zo da su, sun kunshi abinci da amfanin gona da kayayyakin al’adu da sauransu.

Kasar Guinea Bissau ta halarci bikin CIIE a karo na farko a bara, inda ta zo da dangin gyadan kasar don tallata su ga duniya. A cewar jakadan kasar dake kasar Sin, kasar sa na matukar farin-cikin samun damar halartar irin wannan gagarumin biki don gano hajojin da za ta iya fitar da su zuwa kasar Sin, haka kuma za ta iya samun zarafin raya dangantaka tare da sauran kasashe.

A shekara ta 2022, kasar Sin ta ci gaba da bude kofar ta ga kasashen duniya, musamman kasashen Afirka masu tasowa. Tun daga ranar 1 ga watan Disambar bara, Sin ta dakatar da karbar harajin kwastam kan kaso 98 bisa dari, na hajojin wasu kasashe 10, ciki har da Benin, da Burkina Faso, da Guinea Bissau, da Lesotho, da Malawi, da Sao Tome and Principe, da Tanzaniya, da Uganda, da Zambiya, da sauransu. Kana, a watan Yulin bara, an kaddamar da zirga-zirgar jiragen saman dakon kaya tsakanin birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin da birnin Addis Ababa na kasar Habasha, domin jigilar kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Har wa yau, kasar Sin na iya kokarinta don hada kai tare da wasu kasashen Afirka, a fannin yin kirkire-kirkiren sadarwa da gudanar da ciniki ta yanar gizo, a kokarin shigowa da hajojin Afirka cikin kasuwannin kasar Sin.

Shekarar da ta gabata wato 2022, shekara ce mai cike da manyan kalubaloli ga kasar Sin da ma kasashen Afirka, duk da haka, babu wanda zai iya kawo cikas ga huldodin bangarorin biyu. Muna da yakinin cewa, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen Sin da Afirka, hadin-gwiwar su a sabon zamanin da muke ciki, za ta ci gaba da inganta da fadada, har ma za’a kara samar da damammakin ci gaba ga al’ummomin su baki daya. (Murtala Zhang)