logo

HAUSA

Nijeriya na burin kawo karshen shigar da albarkatun man fetur daga ketare zuwa shekarar 2024

2023-01-10 10:37:13 CMG HAUSA

 

Nijeriya na burin kawo karshen shigar da albarkatun man fetur kasar daga ketare, zuwa shekarar 2024, wato a lokacin da ake sa ran matatun mai a kasar za su fara aiki gadan-gadan.

Karamin ministan kula da albarkatun man fetur a kasar, Timipre Sylva, ya shaida yayin wani taron manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, matatar mai ta Fatakwal, wanda yanzu haka ake wa kwaskwarima da matatar mai ta Dangote da ake ginawa da kuma sauran kananan matatun mai na kasar, za su kawo karshen shigar da albarkatun man fetur kasar idan dukkansu suka fara aiki.

Domin tabbatar da wadatar albarkatun mai a cikin gida, gwamnatin kasar ta zuba jarin kaso 20 a matatar mai ta Dangote, yayin da take da jarin kaso 30 a sauran kananan matatun mai na kasar. (Fa’iza)