Masu zuba jari na kasashen waje na da kwarin gwiwar zuba jari a Sin
2023-01-10 10:16:19 CMG HAUSA
Tun daga ran 8 ga wata, Sin ta shiga sabon mataki na kandagarkin COVID-19, abin da ya karawa masu zuba jari a kasashen waje kwarin gwiwa. Wasu kungiyoyin kasuwancin kasashen waje a kasar Sin na ganin cewa, za a dawo da tuntubar mutane da kasuwanci cikin hanzari a tsakanin kasar Sin da kasashen waje. Wasu kamfanonin jarin waje sun nuna cewa, suna tsara shirin ziyarar manyan shugabanninsu zuwa kasar, don ingiza farfado da wasu ayyuka da neman damar zuba jari.
A cikin shekaru 3 da suka gabata, wasu ‘yan siyasar Amurka su kan bayyana ra’ayinsu na rashin gaskiya, da nufin karkatar da wasu harkoki daga Sin. Fuskoki biyu da suka nuna, na fayyace bambancin ra’ayi da suke da shi da nufin dakile kasar Sin. Amma, ba su cimma burinsu a cikin wadannan shekaru ba.
A ran 1 ga wata, Sin ta fara aiwatar da takardar sunayen bangarorin da za a iya zubawa jarin waje. Abin da ya baiwa masu jarin waje damar samun bunkasuwa mai kyau a kasar Sin tare da kawo musu moriya mai armashi. Abin da ba zai yiwu ‘yan siyasa su bata sunansa ba.
Hukumomin tattalin arzikin kasa da kasa sun yi hasashen cewa, Sin za ta samu bunkasuwar tattalin arziki a bana saboda ganin manufofin kandagarki na samun kyakkyawan sakamako tun lokacin da aka shiga sabon matakin kandagarkin annobar. Manazarta sun nuna cewa, ba za a maye gurbin kasar Sin na gaggauta bunkasa tattalin arzikin duniya ba.
Amma, idan an duba tattalin arzikin Amurka, masanan tattalin arziki da masu zuba jari na kasa da kasa sun kai ga matsaya daya cewa, tattalin arzikin Amurka na fuskantar koma-baya. Ya kamata, wasu ‘yan siyasan Amurka su kula da harkokinsu, kada su tsoma baki da shafa bakin fenti kan wasu, kuma ba wanda zai iya siyasantar da tsarin tattalin arziki, kana munafuncin dodo ya kan ci mai shi. (Amina Xu)