logo

HAUSA

Najeriya ta ce a yanzu haka tana da raguwar alluran riga-kafin Covid-19 masu dimbin yawa

2023-01-10 10:08:28 CMG HAUSA

 

Hukumar lura da kiwon lafiya matakin farko a tarayyar Najeriya ta ce a yanzu haka tana da raguwar alluran riga kafin cutar COVID-19 har guda dubu 28.968,045.

Amma duk da haka hukumar ta ce cikin ’yan makonni masu zuwa Najeriya na sa ran samun karin wasu alluran.

Babban daraktan hukumar Dr Faisal Shu’aib ne ya tabbatar da hakan a Litinin din ran 9 ga wata yayin wani taron manema labarai da ma’aikatar lafiyar ta tarayyar Najeriya ta shirya a birnin Abuja.

Babban daraktan wanda ya sami wakilcin Dr Garba Bulama ya ce tun a fakon aikin riga-kafin cutar, an kiyasta yiwa kashi 70 cikin dari na yawan al’ummar Najeriya allurar zuwa watan Disambar 2022.

Amma ya ce daga wancan lokaci zuwa 9 ga watan Janairun wanann shekara ’yan Najeriya 76,161,470 suka amshi matakin farkon na allurar COVID-19, kashi 65.7 ke nan na adadin yawan al’ummar kasar, sai kuma mutum miliyan 66 da suka karbi dukkannin jerin alluran da ake bukata. (Garba Abdullahi Bagwai)