Ministan wajen Sin ya tattauna da takwaransa na Rasha ta wayar tarho
2023-01-10 10:38:47 CMG HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov jiya Litinin, bisa bukatar Lavrov.
Qin ya bayyana cewa, a bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, alaka tsakanin Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani, ta ci gaba da samun bunkasuwa mai inganci, an kuma zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, yayin da goyon bayan abokantakar dake tsakanin kasashen biyu ya ci gaba da ingantu.
Ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, ta ginu ne bisa ka'idar nuna daidaito, da rashin yin fito na fito, da rashin nuna goyon bayan wani bangare. Yana mai cewa, a shirye kasar Sin take ta hada kai da kasar Rasha, wajen aiwatar da muhimman matsayi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da ciyar da dangantakar kasashen biyu zuwa gaba.
A nasa bangare kuwa, Lavrov ya taya Qin Gang murnar zama ministan harkokin wajen kasar Sin, ya kuma bayyana fatansa na kulla kyakkyawar alakar aiki tare da Qin, ta yadda zai jagoranci ma'aikatun harkokin wajen kasashen biyu, wajen ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakaninsu, da aiwatar da muhimmin matsayi da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kuma ingiza cimma sabbin nasarori a cikakkiyar hadin gwiwar dake tsakanin Rasha da Sin. (Ibrahim)
