logo

HAUSA

Kasar Thailand ta yi maraba da zuwan baki masu yawon shakatawa na kasar Sin

2023-01-10 21:55:36 CMG Hausa

Ga yadda jami’an ma’aikatar lafiya, da ma’aikatar harkokin yawon shakatawa da wasanni, da kuma ma’aikatar kula da zirga-zirga na kasar Thailand, suka shirya biki na maraba da zuwan baki masu yawon shakatawa na kasar Sin a filin jiragen sama na Suvarnabhumi, bakin da yawansu ya kai 269, wadanda suka isa kasar cikin jirgin sama na farko da ya sauka a kasar, tun bayan da kasar Sin ta daidaita matakanta na shige da fice.

Kafin dai barkewar annobar Covid-19, yawan baki masu yawon shakatawa daga kasar Sin, ya kasance na farko tsakanin dukkanin baki masu yawon shakatawa da kasar Thailand take karba, adadin da ya zarce miliyan 10 a shekarar 2018. Don haka, kasar Thailand na fatan ganin dawowar bakin kasar Sin za su taimaka ga farfadowar tattalin arzikinta.

Kasashe da dama ma sun bayyana cewa, ba za su dauki matakai na nuna bambanci ga bakin kasar Sin da ke shiga kasashen ba. (Lubabatu)