Hukumar ladaftarwa ta kasar Sin ta sha alwashin aiwatar da ka’idojin taron wakilan JKS
2023-01-10 21:50:57 CMG Hausa
Hukumar koli ta ladaftarwa ta jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS), ta sha alwashin nazarta, tare da aiwatar da ka’idojin aiki da taron wakilan jam’iyyar karo na 20 ya amincewa, kuma hakan zai kasance aikin siyasa da za ta sanya gaba a yanzu, da ma nan gaba.
Hukumar ta bayyana hakan ne, cikin wata sanarwar bayan taro da ta fitar, yayin zama na 2, na hukumar ta sanya ido da ladaftarwa ta 20 ta JKS.