logo

HAUSA

Kasar Sin ta harba sabbin taurarin dan adam uku zuwa sararin samaniya wanda ke zama na farko a shekarar 2023

2023-01-09 10:38:00 CMG Hausa

A yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba sabbin taurarin dan adam guda uku zuwa sararin samaniya a karon farko a sabuwar shekara. 

An harba Taurarin Shijian-23, da Shiyan-22A da 22B ne da misalin karfe 6 na safe agogon birnin Beijing na kasar, ta hanyar amfani da rokar Long March-7A, daga wurin harba kumbuna na Wenchang dake kudancin tsibirin lardin Hainan, inda suka shiga falaki kamar yadda aka tsara.

Galibi ana amfani da tauraron dan adam na Shijian-23 ne wajen yin gwaje-gwajen kimiyya da tabbatar da fasaha, yayin da taurarin adam Shiyan-22A da 22B kuma, ake amfani da su wajen gudanar da gwaje-gwajen tabbatar na sabbin fasahohi a aikin binciken sararin samaniya, kamar sa ido kan yanayin sararin samaniya. 

Wannan shi ne karo na 459 da aka yi amfani da rokar Long March wajen harba taurarin dan-adam zuwa sararin samaniya. (Ibrahim Yaya)