logo

HAUSA

Labarin wasu 'yan mata Sinawa da suka kyautata zaman rayuwarsu ta hanyar samun ilmi

2023-01-09 20:47:50 CMG Hausa

A ranar 11 ga watan Oktoban 2021, ranar 'ya'ya mata ta duniya karo na 10. Madam Peng Liyuan, manzon musamman ta Shirin Spring Bud, mai rajin inganta ilimin 'ya'ya mata a kasar Sin, ta sanar da kaddamar da shirin Dream of the Future Action, domin yayatawa da aiwatar da shirin wanda ke karkashin Shirin Spring Bud. A ranar 7 ga watan Junairun 2022, asusun kula da kananan yara da matasa 'yan kasa da shekaru 20 na kasar Sin (CCTF), ya kaddamar da wani shirin raya ilimin 'ya'ya mata a yankin Liangshan, a makarantar midil ta Xining dake yankin Liangshan na kabilar Yi mai cin gashin kansa dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, inda aka bayar da gudunmuwar kudi da kayayyakin da darajarsu ta kai yuan miliyan 48, kwatankwacin dala miliyan 7.06, domin taimakawa 'yan matan Liangshan. A matsayin wani muhimmin bangare na shirin Spring Bud, shirin Dream of Future Action, zai ci gaba da tallafawa ilimin 'ya'ya mata da dukkan ayyukan raya yankin Liangshan.

Liangshan, inda tsaunin Daliangshan yake, mazauni ne mafi girma na 'yan kabilar Yi a kasar Sin. akwai mazauna miliyan 4.86, inda fiye da rabinsu suka kasance 'yan kabilar Yi.

A baya, 1 bisa 4 na 'yan matan da suka kai matakin shiga makaranta ne kadai suke karatun firamare, kuma kalilan daga cikinsu ne ke kammala makarantar firamare. Adadi mai yawa na 'yan matan ne ke barin makaranta.

A 1992, da taimakon Margaret Chow Kit Bing daga yankin Hong Kong na Sin, asusun CCTF ya kaddamar da ajujuwan 'yan mata karkashin shirin Spring Bud, a gundumar Butuo ta Liangshan, domin taimakawa 'yan matan kabilun Yi da Miao da sauran wasu kabilun da suka bar makaranta, sake komawa aji.

Tun bayan kaddamar da shi da asusun CCTF ya yi a 1989, Shirin Spring Bud, ya samar da gudunmuwar sama da yuan biliyan 2 da miliyan 586, kwatankwacin dala miliyan 380, kuma an yi amfani da kudin ne wajen taimakawa 'yan mata sama da miliyan 3.96 samun ilimi da cimma burikansu, cikinsu har da wadanda suke Liangshan.

Jidi Moshiliu, daya daga cikin 'yan mata na farko da suka kammala karatu daga ajin 'yan mata na Shirin Spring Bud a gundumar Butuo, yanzu malama ce a makarantar firamare ta Temuli dake garin Temuli na gundumar Butuo.

Ta fara karatun firamare ne a lokacin da take da shekaru 7. A lokacin, ita ce kadai 'yar kabilar Yi cikin dalibai kusan 50 dake ajinsu. Ta bar makaranta ne bayan shekaru hudu da ta fara karatun. A wata rana a watan Satumban 1992, sakataren reshen JKS na kauyensu, ya ziyarci gidansu Jidi, inda ya ce Jidi za ta iya komawa makaranta da taimakon Shirin Spring Bud. Iyayenta sun yi farin ciki da jin wannan labari.

“Ina son zama malama,”Jidi ta tabbatarwa kanta a ranar farko da ta shiga aji. Ta yi farin cikin samun damar komawa karatu, inda ta jajirce. Bayan ta kammala makarantar midil, sai ta samu gurbin karatun a wata kwalejin koyar da ilmin koyarwa.

Jidi ta zama malama a firamaren Temuli ne a shekarar 2006, bayan ta kammala karatun kwalejin. Tana kaunar aikinta. Ta ce tana kasancewa cikin tsananin farin ciki idan ta kalli dalibanta a makaranta.

Jidi ce kadai malama mace daga kauyensu. Cikin shekaru 30 da suka gabata, ta shaida sauye-sauyen da aka samu a kauyen. Misali, kauyen ya kafa makarantar rainon yara, kuma rayukan mazauna na ci gaba da ingantuwa.

Ta yi ammana cewa, galibin sauye-sauyen da aka samu a kauyen sakamako ne na aiwatar da Shirin Spring Bud. Ta ce tana fatan dukkan yaran yankin tsaunin Daliangshan za su samu ingantaccen ilimi, da sauya makomarsu ta hanyar samun ilimi.

An haifi Wang Fumei a kauyen Yizi a shekarar 1977, 'yar asalin kabilar Miao dake can cikin tsaunin Daliangshan. Ta fara karatun firamare ne lokacin da take da shekaru 9, amma ta bar makaranta daga bisani. Iyayenta na rayuwa cikin yanayi na wahala, kuma dole ta taimaka musu da ayyukan gona.

A wata rana a watan Agustan 1992, Wang ta ji labarin Shirin Spring Bud. Sai dai, iyayenta ba su so ta koma makaranta ba. Sai mambobin kungiyar mata da kuma malamai suka lallashi mahaifiyarta, domin ta ziyarci makarantar, da kuma ajin 'yan mata na Spring Bud. A karshe dai mahaifiyarta ta amince ta koma makaranta.

A lokacin, akwai ajujuwa 2 a gundumar Butuo, daya a firamaren Temuli, dayan kuma a makarantar Xixihe. A karshe, Wang ta fara zuwa ajin makarantar Xixihe.

A 1996, Wang ta samu gurbin karatu a makarantar sakandare ta nazarin ayyukan rediyo da talabiji na Sichuan, domin koyon ilmin hada-hadar kudi. Bayan ta kammala, ta ci jarrabawar zama ma'aikaciyar gwamnatin gundumar Butuo, ta kuma yi aiki da sassan gwamnati a wasu garuruwan wurin. Yanzu ita ce mataimakiyar shugaban garin Temuli.

Yayin da take aiki a garin Dala, ita ce mai kula da ayyukan yaki da talauci a kauyen Boshi na kabilar Yi. A 2016, kudin shigar kowanne mazaunin kauyen a shekara, bai kai yuan 3,000 ba, wato dala 441. Amma da taimakon gwamnati da kokari irin na Wang Fumei da mutanen kauyen, kudin shigarsu ya karu zuwa sama da yuan 4,300, kwatankwacin dala 632 a cikin shekaru 3, ta hanyar shuka bishiyoyin kayan marmari da gyadar walnut da sauransu.

Wang Fumei ta kuma shiryawa matasan kabilar Yi horon koyon sana'o'i, kana ta karfafa musu gwiwar aiki a yankunan dake wajen tsaunin Daliangshan, domin su kara bude ido.(Kande Gao)