logo

HAUSA

Kasashen duniya na kokarin jan hankalin Sinawa matafiya bayan sake bude iyakokin kasar Sin

2023-01-09 11:28:48 CMG Hausa

Kasashe a fadin duniya na murna dangane da tsammanin miliyoyin Sinawa masu tafiye-tafiye, bayan dage dokar takaita tafiye-tafiye a kasar.

A jiya Lahadi, 8 ga wata ne aka dage dokar takaita tafiye-tafiyen da aka ayyana shekaru 3 da suka gabata biyo bayan barkewar annobar COVID-19. Sassauta dokar na zuwa ne a daidai lokacin da bikin bazara ta sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ke karatowa. Akwai yuwuwar Sinawa za su yi biliyoyin tafiye-tafiye a cikin gida da ma kasashen waje, yayin bikin na kwanaki 7 da za a fara daga ranar 21 ga wata.

Gwamnatoci a fadin duniya ba su tsaya bata lokaci ba wajen jan hankalin Sinawa matafiya saboda sassauta dokar a jiya, inda suka yi ta wallafa hotuna da bidiyon fitattun wuraren yawon shakatawa a shafin Weibo, wanda yake tamkar shafin Twitter a kasar Sin.

Bayanai sun bayyana cewa, gangamin jan hankalin matafiya ya zo a kan gaba, bisa la’akari da karuwar bukatar tafiye-tafiye saboda zuwan bikin bazara. (Fa’iza Mustapha)