logo

HAUSA

PLA ta gudanar da atisaye a kusa da tsibirin Taiwan don magance takala

2023-01-09 10:35:21 CMG Hausa

Rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin PLA reshen gabashin kasar, jiya Lahadi ta gudanar da wani sintiri da atisayen yaki na hadin gwiwa a kewayen tsibirin Taiwan. 

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiyan, mai mgana da yawun rundunar reshen gabashin kasar, babban kanar Shi Yi, ya ce sun dauki wannan mataki ne, a matsayin martani ga takalar dakarun waje da kuma na Taiwan dake neman ’yancin kai.. 

Shi ya bayyana cewa, atisayen hadin gwiwa na shirye-shiryen yaki a cikin ruwa da sararin samaniyar tsibirin, ya hada da dakaru na sassa da dama, kuma an tsara shi ne don gwada yadda za a kai hare-hare ta kasa da ta ruwa. 

Atisayen dake zama na irinsa na farko a shekarar 2023, na zuwa ne bayan da wani makami mai linzami samfurin USS Chung-Hoon ya ratsa ta mashigin Taiwan a ranar 5 ga watan Janairu. (IbrahimYaya)