logo

HAUSA

Albishiri ga masu son kawo ziyara kasar Sin

2023-01-09 17:35:59 CMG Hausa

Abokaina, albishirin ku, Ina fatan za ku ce GORO. Madalla. Ku karkade kunnuwanku... sanin kowa ne cewa, kasar Sin ta gyara manufarta ta kandaganrkin yaduwar cutar COVID-19 a kwanan baya, wadda ta kunshi daidaita ka’idojin shigi da fici. Tun daga ranar 8 ga watan da muke ciki,  duk masu son shigowa Sin daga kasar waje, zai yi gwajin cutar COIVD-19 sa’o’i 48 kafin ya bar kasarsa, daga baya idan ya samu sakamakon ba ya dauke da cutar, to zai iya shiga kasar Sin kai tsaye, sa’an nan babu bukatar killacewa bayan ya shiga kasar.

Cikin shekaru 3 da suka wuce, yayin da annobar COVID-19 ke addabar al’ummar duniya, gwamnatin kasar Sin ta tsaurara matakan kandagarkin yaduwar cutar a bangaren shigi da fici, bisa manufarta ta dora matukar muhimmanci kan rayukan jama’a, da yin la’akari da hakikanin yanayin da kasar ke ciki a fannin dakile annobar. Matakan da suka hada da yi wa mutanen da suka shigo kasar Sin gwaji na COVID-19 bayan sun iso, da killacewa don magance yaduwar cutar, da dai sauransu. Wadannan matakai sun taka muhimmiyar rawa a kokarin kasar na dakile cutar COVID-19, duk da haka suna da nasu illar, wato matakan sun haifar da shinge ga cudanyar al’ummar Sinawa da na ragowar kasashen waje.

Sai dai a halin yanzu saboda raguwar karfin illar da kwayoyin cutar COVID-19 ke haifarwa, kana fiye da kashi 90% na al’ummar kasar Sin sun karbi cikakkun alluran rigakafin cutar, yayin da kasar ita ma ta samu ci gaba sosai a fannin kirkiro magunguna da adana isashen kayayyakin da ake bukata don jinyar mutanen da suka kamu da cutar COVID, suka sa kasar Sin samun damar daidaita manufarta ta dakile annoba, tare da saukaka matakan shigi da fici.

Cikin shekarun 3 da suka wuce, wasu abokaina dake Najeriya da Nijar su kan tambaye ni, “Yaushe kasar Sin za ta saukaka matakanta na shiga kasar?” ko kuma “Zuwa yaushe zan iya zuwa kasar Sin don sayen kayayyaki?” kasancewarsu ‘yan kasuwa, wadanda suka saba zuwa biranen kasar Sin irinsu Guangzhou da Yiwu don sayen kayayyakin da suke bukata, kana kafin barkewar annobar COVID su kan ziyarci kasar Sin sau 3 zuwa 4 a shekara. Sai dai cutar COVID-19 ta sa shiga kasar Sin zama wani aiki mai wuya, don haka sun fara karkata ga yanar gizo ta Internet don sayen kayayyaki. Amma yin ciniki ta yanar gizo shi ma yana da wuya. Kamar yadda wani abokina dan kasuwa ya fada, “ Sai an buga waya kusan sau fiye da goma, da aike da sakonnin E-mail fiye da dari, kuma hakan bai kai yadda za a yi magana gaba cikin ‘yan mintuna ba.” Masu iya magana na cewa, zuwa da kai, ya fi aike. Ban da wannan kuma yadda aka dakatar da zirga-zirgar jiragen sama sakamakon samun fasinjoji da suka kamu da COVID a kai a kai, da hauhawar farashin hidimar jigilar kayayyaki, dukkansu sun haifar ma ‘yan kasuwan da matsaloli.

Ko da yake cinikin kasa da kasa a wadannan shekaru ya gamu da matsala, kana tattalin arzikin duniya na ci gaba da tafiyar hawainiya, amma cinikin da ake yi tsakanin Sin da Afirka na ta samun karuwa. Ko a watanni 6 na farko na shekarar 2022 kadai ma, darajar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 137.4, jimillar da ta karu da kashi 16.6% idan an kwatanta da ta makamancin lokacin shekarar 2021. Inda darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 60.6, adadin da ya karu da kashi 19.1% bisa na makamancin lokacin shekarar 2021. Duk wadannan karuwa an same su ne a wani lokacin da ake fuskantar matsala a fannin shigi da fici na kasar Sin. Saboda haka, ana iya kyautata zaton cewa, bayan da aka saukaka matakan kayyade shigi da fici, ‘yan kasuwan kasashen Afirka da na kasar Sin za su samu damar gudanar da karin ziyarar aiki, da cudanya da juna fuska da fuska, lamarin da zai sanya adadin cinikin Sin da Afirka karuwa sosai.

Wannan karuwar cinikayyar za kuma ta sa kasashen Afirka samun karin kudin shiga a fannin harajin kwastam, da kudin da ‘yan kasashen suke aikewa gida, ta yadda hakan zai saukaka matsin lamba ga tattalin arziki. Haka zalika, karuwar ciniki za ta sanya kudin da ake kashewa a fannonin jigilar kayayyaki da adana su ya ragu, ta yadda ‘yan kasuwan kasashen Afirka za su samu karin riba, kana jama’ar kasashe daban daban dake nahiyar Afirka su ma za su samu damar samun kayayyaki masu araha da inganci. Ban da wannan kuma, kamar yadda kasar Kenya ta fara sayar da ’ya’yan marmari na Avocado zuwa kasar Sin a watan Agustan bara, karin kayayyakin kirar kasashen Afirka za su samu damar shiga cikin kasuwannin kasar Sin, don baiwa kasashen da suke samar da su riba da karin guraben aikin yi.

Ba shakka amfanin daidaita matakai masu alaka da shigi da fici bai tsaya ga bangaren ciniki kawai ba, ganin yadda farfadowar cudanyar mutanen kasashen Afirka da na kasar Sin za ta haifar da ci gaban harkokin zuba jari, da yawon shakatawa, da al’adu, da aikin samar da ilimi, da dai sauransu. Yadda kasar Sin ta daidaita manufarta a fannonin kandagarkin cutar da aikin mai alaka da shigi da fici, ta nuna wa kasashen duniya cewa, “An yi ban kwana da lokaci mai wahalar gaske, yanzu lokaci ya yi da ya kamata a hada hannu don samun cikakkiyar farfadowa daga illar da annobar COVID-19 ta haifarwa duniyar bil-Adama.” (Bello Wang)