logo

HAUSA

Burundi ta nemi agajin Najeriya a bangaren samar da makamashi musamman man fetur

2023-01-09 09:55:12 CMG Hausa

A ranar 8 ga wata ministan kudi da tsare-tsare na kasar Burundi Mr Audace Niyonzima ya gana da shugaban kasar tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa dake birnin Abuja.

Yayin ziyarar, ministan ya nemi agajin Najeriya a bangaren makamashi musamman batun man fetur.Ya ce, karancin mai na mutukar ciwa kasar tuwo a kwarya.

Da yake nasa jawabin, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba bisa wannan ziyara, sannan ya yi alkawarin cewa zai tuntubi babban kamfanin samar da mai na kasar  domin duba hanyoyin da za a taimakawa kasar ta fuskar man fetur. Ya ce ya san irin mawuyacin yanayin da kasar Burundi ke shiga a duk lokacin da ta fuskanci karancin makamashi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jaddada kudirin gwamnatinsa na taimakawa kasar ta Burundi a dukkan fannoni na rayuwa, domin kamar yadda shugaban ya ce Najeriya na daukar duk wata kasa ta Afrika a matsayin aminiya ta hakika. (Garba Abdullahi Bagwai)