logo

HAUSA

Amurka ba ta cancanci zargin wasu sassan ba bayan ta gaza shawo kan COVID-19 a cikin gida

2023-01-08 20:51:26 CMG Hausa

Tun daga yau Lahadi, kasar Sin ta sassauta matakanta na yaki da cutar COVID-19 daga rukunin A zuwa rukunin B, don haka ta daina daukar matakan binciken cutar kan matafiya da kayayyaki dake shigowa daga ketare, an kuma dawo da yawon bude ido na 'yan kasar Sin zuwa ketare yadda ya kamata.

Kasar Sin ta shafe shekaru uku tana shirye-shirye domin wannan rana. Bayan da ta yi ta fama da ayyukan yaki da cutar, kasar Sin ta inganta manufofin kandagarkin annobar bisa lokaci da yanayin da ake ciki, wanda hakan zai taimaka wajen daidaita aikin rigakafin cutar, da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma, haka kuma zai taimaka wajen yin mu’amalar al’ummar kasar Sin da na kasashen waje.

Amma duk da haka, yanzu wasu 'yan siyasa da kafofin watsa labaru na Amurka wadanda a baya suka yi kira ga kasar Sin da ta sassauta manufarta ta yaki da cutar sun soma sukar daidaita manufofin kandagarkin cutar da kasar Sin ta yi, inda suke sanya takunkumi ga shigar baki masu yawon bude ido daga kasar Sin kasar su. Irin wannan mataki da suka dauka bisa ma’aunai biyu, ya fallasa duhun tunaninsu, kan nasarorin da Sin ta samu wajen yaki da annobar.

A halin yanzu, nau’ikan cutar iri-iri na yaduwa a Amurka, hakan ya sa mutanen kasar ke shan wahala kwarai. Maimakon yin la'akari da yadda suka yi sakaci da aikinsu, wadannan 'yan siyasar Amurka, suna ta kokarin bata sunan kasar Sin a fannin yaki da annobar, tare da rika siyasantar da annobar, don kawar da tunanin al’umma game da sabanin dake cikin kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)