logo

HAUSA

Halin rigakafin annoba a Amurka yana da ban tsoro, ta yaya za ta nuna yatsa ga saura?

2023-01-08 14:15:49 CMG Hausa

Bisa kididdigar da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta fitar, kasar Amurka ta fuskanci bala'in annobar COVID-19 har sau biyar a cikin shekaru uku da suka gabata. Kuma a duk lokacin da adadin masu kamuwa da cutar ya kai matsayin koli, ana samun rahotanni masu yawa, game da yadda ake samun kusan rugujewar tsarin aikin likitancin kasar.

Sakamakon sakaci da aiki da gwamnatin Amurka ke yi, kusan dukkanin nau'ikan cutar COVID-19 sun taba yaduwa a kasar, wanda hakan ya haddasa harbuwar mutane sama da miliyan 100 a kasar, kana sama da mutane miliyan 1.08 sun mutu, baya ga yara 250,000 da suka zama marayu saboda kisan da annobar ta yi, inda matsanancin halin da kasar ke ciki ya sanya ta kan gaba a fannin fama da cutar a duniya.

Wasu manazarta sun yi nuni da cewa, ainihin abin da ya haifar da yanayin da ake ciki shi ne, yadda gwamnatin Amurka ba ta taba sadaukar da karfinta ga aikin magance hakikanin matsalolin da take da fuskanta ba, maimakon hakan tana ta siyasantar da batun annobar.

Sabanin haka, kasar Sin ta aiwatar da matakai daban daban a cikin shekarun ukun da suka gabata, inda ta aiwatar da tsauraran manufofin rigakafi, da shawo kan cutar a lokacin da ake shan fama da ita, ta jure jarrabawar yaduwar annobar har sau biyar, kana da rage yawan wadanda suka nuna alamu masu tsanani ko kuma mace-mace a sakamakon cutar. Har ila yau, ta samu lokaci mai muhimmanci na nazarin magunguna, da alluran rigakafin cutar.

Kamar sauran kasashe, kasar Sin ma na bukatar wani lokaci na daidaitawa, wajen kyautata manufofin rigakafin cutar. Musamman yadda kasar Sin ke da yawan al’umma da yawan tsofaffi, don haka babu makawa, kasar na fuskantar wasu matsaloli, ciki har da karuwar adadin masu kamuwa da cutar, da masu bukatar magani.  Amma duk da haka, gwamnatin kasar Sin ba ta taba yin kasa a gwiwa ba, wajen sanya himmar warware matsalolin ta. Bugu da kari, a cewar mai tsara shirye-shiryen documentary dan kasar Burtaniya Malcolm Clarke, wanda ya taba zama a kasar Sin tsawon shekaru uku da suka gabata, “Na kasance mai cin gajiyar kokarin da Sin ke yi na kare rayuka da lafiyar jama'a.”

Daga yau 8 ga watan Janairu na shekarar bana, kasar Sin ta sassauta matakanta na yaki da cutar COVID-19 daga rukunin A zuwa rukunin B, don haka ta daina daukar matakan binciken cutar ba kan matafiya da kayayyaki dake shigowa daga ketare. Wannan shi ne kokarin da kasar Sin ta yi na baya-bayan nan, don inganta manufofin kandagarkin annobar bisa lokaci da yanayin da ake ciki, wanda hakan sauke nauyin al'ummar kasar ne, kuma yana taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)