logo

HAUSA

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu matafiya dake cikin jirgin kasa a jihar Edo ta Najeriya

2023-01-08 15:47:36 CMG Hausa

A jiya Asabar ne rundunar ’yan sandan jihar Edo dake shiyyar kudu maso kudancin Najeriya, ta sanar cewa, wasu‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu fasinjojin jirgin kasa da dama, a lokacin da suka taso daga karamar hukumar Igueben zuwa Warri dake jihar Delta.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar Chidi Nwabuzor, ta yi bayanin cewa, al`amarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin jiya Asabar.

Kamar yadda sanarwar ta yi bayani, masu garkuwa da mutanen dauke da bindigogi kirar AK47, sun kutsa kai cikin jirgin, inda suka fara harbin iska, kafin daga bisani su yi awon gaba da fasinjoji da dama zuwa cikin daji.

A yayin wannan farmaki, kamar yadda kakakin ’yan sandan ya bayyana, wasu daga cikin fasinjojin da suka tsira sun sami raunuka sanadiyar harbin bindiga.

A yanzu haka dai rundunar ’yan sandan ta kaddamar da aikin sassare bishiyoyin dake cikin dajin da ’yan bindigar suke fakewa, a kokarin tabbatar da ganin an ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.  (Garba Abdullahi Bagwai)