logo

HAUSA

Mutane 14 sun mutu sanadiyar kifewar kwale-kwale a Najeriya

2023-01-07 15:42:38 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 14 ne suka mutu, wasu 6 kuma suka bace, bayan da wani kwale-kwale da suke ciki ya kife a farkon makon nan a yankin arewa maso yammacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito a jiya cewa, kimanin manoman shinkafa 100 ne ke cikin kwale-kwalen a lokacin da ya kife da yammacin ranar Talata, a kan wani kogi da ke karamar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi, koda yake an yi nasarar ceto mutane 80 da ransu.

Wata sanarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar a jiyan, ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, ya kuma yaba da kokarin ma’aikatan ceto, wadanda a cewarsa, sun shafe kwanaki suna aikin neman wadanda suka bata.

Shugaba Buhari ya bukaci masu ruwa da tsaki, da su mai da hankali kan ka’idojin tafiyar da sufurin kwale-kwale yadda ya kamata, musamman a yankunan karkara.(Ibrahim)