logo

HAUSA

WHO: sauyin yanayi ya haddasa tsanantar matsalar lafiya a yankin kahon Afirka

2023-01-07 23:24:37 CMG Hausa

Kwanan baya, ofishin kula da harkokin Afirka karkashin inuwar hukumar lafiya ta kasa da kasa wato WHO ya shirya taron manema labaru ta kafar internet a birnin Brazzaville na kasar Congo(Brazzaville), inda ya yi karin bayani kan yadda sauyin yanayi ya haifar da matsalar lafiya a yankin kahon Afirka ko Horn of Africa a Turance, musamman ma barkewar cututtuka sau da dama.

Alkaluman WHO sun nuna cewa, matsalar lafiya da sauyin yanayi ya haifar a yankin kahon Afirka, ta riga ta shafi baki dayan yankin, wato kasashen Djibouti, Habasha, Kenya, Somalia, Sudan ta Kudu, Sudan da Uganda. Fari da ambaliyar ruwa da sauyin yanayi ya haddasa sun jefa mazauna yankin miliyan 47 cikin tsananin yunwa, tare da haifar da barkewar matsalolin lafiyar al’umma, kamar cututtukan anthrax, kyanda, kwalara, shawara, da Ebola. Mummunan yanayi ya sanya ‘yan Adam da namun daji suna rayuwa tare a wasu yankuna, lamarin da ya haddasa barkewar annobar Ebola da wasu sauran cututtukan da dabbobi ke yadawa bil Adama.

Dakta Patrick Otim, jami’in WHO mai kula da harkokin rigakafi da daidaita batutuwan ba zata ya nuna cewa, sauye-sauyen zafin yanayi da sauyin yanayi sun sanya dabbobi masu dauke da kwayar cutar ta Ebola sun kaura zuwa wani wuri na daban. A kan samu kwayar cutar Ebola da wasu sauran kwayoyin cutuka na musamman a jikin jemage. An yi fama da fari a wuraren da wadannan dabbobi ke rayuwa a baya, ba su ci gaba da zama a wadannan wurare ba, don haka su kan kaura zuwa wasu wurare masu ni’ima, inda watakila ‘yan Adam su ma suke zama. Ta haka wadannan dabbobi da ‘yan Adam suke rayuwa tare a wasu wurare, lamarin da ya haifar da barkewar cutar Ebola sau da dama a wadannan wurare.

A cikin shekaru 5 da suka wuce, yawan mutanen da ke fama da matsalar yunwa a yankin kahon Afirka ya ninka fiye da sau 1, lamarin da ya tsananta illolin da cututtuka da matsalar karancin abubuwa masu gina jiki suke haifarwa juna. Wasu masu fama da cutuka suna fuskantar matsalar karancin abubuwa masu gina jiki, yayin da wadanda ke fama da matsalar karancin abubuwa masu gina jiki suka fi fuskantar hadarin kamuwa da cutuka da kuma mutuwa.

WHO ta yi kira da a inganta kiyaye masu rauni yayin da ake fuskantar lalacewar matsalar lafiya, musamman ma tabbatar da bai wa kananan yara hidimomin lafiya, a kokarin samar da isasshen abubuwa masu gina jiki.  (Tasallah Yuan)