logo

HAUSA

‘Yan tawayen M23 sun janye daga sansanin soji da suka kwace a arewa maso gabashin DR Congo

2023-01-07 15:37:00 CMG Hausa

A jiya ne, 'yan tawayen M23, suka mika sansanin soji na Rumangabo da suka kwace a yankin arewa maso gabashin kasar Congo Kinshasa a watan Oktoba ga sojojin kungiyar raya kasashen gabashin Afrika (EAC) a hukumance.

An gudanar da bikin mika sansanin soji mai tazarar kilomita 40 daga birnin Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa ne, a gaban jami'an rundunar yankin EAC, da tawagar tabbatar da hadin gwiwa ta manyan tabkuna, da jagororin ‘yan tawayen M23.

Mataimakin kwamandan rundunar EAC mai kula da yankin, Emmanuel Kaputa, ya ce, bikin ya nuna ci gaba da gudanar da wani aiki da tuni aka fara aiwatarwa, kafin janyewar 'yan tawayen daga garin Kibumba a watan Disambar 2022.

A ranar 23 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, 'yan tawayen suka janye daga Kibumba, kimanin kilomita 20 daga Goma, a matsayin " nuna fatan alheri da aka yi da sunan samar da zaman lafiya.(Ibrahim)