logo

HAUSA

Hukumar cudanya da jam’iyyun siyasa na ketare ta kwamitin kolin JKS ta yi bayani kan yadda kasar Sin ke yin rigakafi da shawo kan annobar COVID-19

2023-01-06 12:04:35 CMG Hausa

Hukumar cudanya da jam’iyyun siyasa na ketare ta kwamitin kolin JKS, ta aike da wasiku ga jam’iyyun siyasa, da kungiyoyin siyasa na kasashen waje, inda ta bayyana abubuwan da aka yi la’akari da su wajen sauya manufofin rigakafi da shawo kan annobar COVID-19 a Sin, da kuma ma’ana mai amfani ta karfafa hadin gwiwa, da mu’ammala tsakanin kasashen duniya kan hakan.

Hukumar ta ce domin dacewa da sabon yanayin rigakafi, da matakan shawo kan annobar, da kuma sabuwar nau’in kwayar cutar, kasar Sin ta kyautata manufofin rigakafi da shawo kan cutar, da nufin kula da rigakafi da shawo kan cutar, da kuma inganta bunkasuwar zamantakewa da tattalin arzikin al’umma, da dai kiyaye rayukan jama’a da ayyukan su yadda ya kamata, aikin da ya zama dole, ya kuma dace da ilimin kimiyya, kuma an yi shi kan lokaci.

A cikin shekaru uku da suka gabata, ayyukan kawar da cutar da Sin ta gudanar, ya aza tubali na kyautata manufofin rigakafi da shawo kan cutar, kuma akwai kwarin gwiwa game da samun nasarori a dukkan fannoni, game da shawo kan cutar.

Hukumar ta kara da cewa, sauyin nau’in cutar a Sin, zai samar da sabbin muradun ga zirga-zirgar Sinawa, da al’ummun kasashen waje cikin tsari, da kuma ci gaban zamantakewar tattalin arzikin kasashen dumiya. Har ila yau, jam’iyyar kwaminis ta Sin, na son kiyaye yanayin hadin gwiwa na shawo kan cutar bisa tsari a dukkanin sassan duniya, da hada hannu don gina al’ummar bai daya a fannin kiwon lafiya, da kuma al’umma da makomar bai daya ta bil adama, tare da jam’iyyun siyasa na dukkan kasashen duniya. (Safiyah Ma)