An yi hasashen tafiye-tafiyen fasinjoji a bikin bazara na Sin zai karu da kashi 99.5
2023-01-06 20:52:43 CMG Hausa
Mataimakin ministan sufuri na kasar Sin Xu Chengguang, ya shaidawa manema labarai Jumma'ar nan cewa, ana hasashen jimillar tafiye-tafiyen fasinjoji a kasar, a lokacin bikin bazara na bana, zai karu da kashi 99.5 bisa dari kan na shekarar 2022, zuwa kusan biliyan 2.095.
Ya bayyana cewa, balaguron hutun na bana, daga ranar 7 ga watan Janairu zuwa 15 ga Fabrairu, kusan tsawon kwanaki 40, shi ne mafi sarkakiya da kalubalen tafiye-tafiye, wanda ke cike da rashin tabbas sakamakon cutar COVID-19 da kuma yawan matafiya. (Ibrahim)