logo

HAUSA

OCHA: An tallafawa sama da mutane miliyan 3.3 da agajin jin kai a yankin Tigray na kasar Habasha

2023-01-06 11:25:06 CMG Hausa

Ofishin tsara ayyukan jin kai na MDD ko OCHA a takaice, ya ce tsakanin farkon watan Oktoban shekarar da ta shude zuwa yanzu, al’ummun Tigray dake yankin arewa mai nisa na kasar Habasha, wadanda yawan su ya kai sama da miliyan 3.3 sun karbi agajin jin kai da ofishin ke samarwa.

OCHA ya ce ana kai kayayyakin agajin ne ta jiragen sama, tun bayan da aka sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin dakarun gwamnatin Habasha da mayakan kungiyar dake rajin ‘yantar da yankin Tigray ko TPLF, a farkon watan Nuwambar bara.

Yarjejeniyar dai ta kunshi sake dawo da doka da oda, da baiwa ma’aikatan ba da agaji damar shigar da kayayyaki, da hidimomi ga  masu bukata ba tare da wani shinge ba.

Tuni dai aka maido da hidimomin wayar tarho da wutar lantarki, yayin da kuma ake ci gaba da kyautata samar da muhimman ababen more rayuwar jama’a, da suka hada da ruwa mai tsafta, a birane da dama dake yankin na Tigray, wanda a baya ya sha fama da yaki. (Saminu Alhassan)