logo

HAUSA

Sin ta yi imani da karfin jama’ar Habasha na magance harkokinsu da kansu

2023-01-06 21:06:01 CMG HAUSA

 

Rahotanni daga yankin Tigray na kasar Habasha na cewa, al’amura na inganta a baya-bayan, inda sannu a hankali aka dawo da ayyuka na yau da kullum kamar ruwa da wutar lantarki da sadarwa da jin kai da sufurin jiragen sama, baya ga ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma. Game da hakan, a yayin taron manema labarai na yau da kullum da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya Juma’ar nan, mai magana da yawun ma’aikatar Mao Ning ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Habasha da kungiyar ‘yantar da jama’ar Tigray, suna kokarin tabbatar da yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma, inda aka yi nasarar maido tsarin zamantakewa da tsaro a jihar, Sin na maraba da hakan tare da yiwa musu fatan alheri.

Mao Ning ta ce, dangane da rikici cikin gidan kasar Habasha, Sin tana kan matsayin na adalci, kuma tana da imanin cewa, jama’ar Habasha na da hikima da karfin magance rikicin cikin gidansu, Sin tana nacewa ga mutunta ‘yanci da cikakken yankunan kasar da goyon bayan kokarin da gwamnati da jama’a suke yi na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da bunkasuwa. Ban da wannan kuma, a ko da yaushe, Sin tana goyon bayan al’ummar Afirka da su warware matsalolinsu da kansu, da ma goyon bayan AU ta taka rawa mai kyau don magance matsalolin. (Amina Xu)