logo

HAUSA

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta karbi kason karshen na na’urorin kada kuri’a da ta yiwo oda daga waje

2023-01-05 14:57:10 CMG Hausa

 

A jiya Laraba 4 ga wata hukumar zaba mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta karbi kason karshe na na’urar kada kuri’a da tantance masu zabe wadda ake kira da BVAS.

Wata sanarwar da kwamashinan hukumar mai lura da wayar da kan masu zabe Mr Festus Okoye ya rabawa manema labarai ya yi bayanin cewa, shugaban hukumar Farfessa Mahmood Yakubu tare da wasu manyan jami’an hukumar ne suka karbi kayan a babban filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Abuja .

Mr Festus Okoye ya ce hukumar ta kebe manyan filayen jiragen sama 4 da za su kasance cibiyoyin da za a yi amfani da su wajen rarraba na’urorin zuwa sassan kasar .

Filaye da aka kebe kuwa sun hada da babban filin jirgin sama na Kano da Legos da Abuja da kuma Fatakwal.

Yau sama da watanni 4 ke nan jiragen sama ke ta sintirin raba na’urorin BVAS zuwa jihohi a dai dai lokacin da ya rage kasa da kwanaki 50 a gudanar da babban zabe a kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)