logo

HAUSA

A matsayinta na kasa mafi yawan masu harbuwa da cutar COVID-19 a duniya, matakin Amurka, tamkar “Barawo ke cewa ku tare barawo!"

2023-01-05 11:11:01 CMG Hausa

Tun daga ranar 5 ga watan nan na Janairu, Amurka ta sanyawa masu yawan shakatawa daga Sin takunkumin shiga kasar, saboda barkewar cutar a cikin gidan Sin, bisa zargin cewa wai "Shigar da Sinawa Amurka na iya haifar da bullar sabbin nau'o’in cutar, wanda ka iya haifar da hadarin yaduwar cutar."

To sai dai kuma bisa shaidun kimiyya kan kwayoyin cutar, kwayar cutar mafi yawa a cikin Sin ita ce nau’in BA.5, wadda babbar kwayar cuta ce da aka samu a Amurka a watannin baya bayan nan, yayin da kwayar cutar XBB.1.5 da aka samu a yankin Shanghai da Hangzhou, ta kasance babbar kwayar cuta mafi yaduwa a Amurka. Don haka dai, ana iya gane cewa, kasar Sin na fama da annobar cutar a duniya, yayin da Amurka ta yi watsi da gaskiyar lamarin, ta kuma saba wa kimiyya, bisa wani shirin siyasa na “Barawo ke cewa ku tare barawo”.

Bisa kididdigar cibiyar lura da cutar mura ta Duniya, an gano cewa, nau’in XBB.1.5 na COVID-19 ya yadu a kasashe da yankuna a kalla 74, ciki har da jihohi 43 na Amurka. Yawancin masana Amurkawa sun nuna cewa, samfurin farko da aka gano na XBB.1.5, an same shi a biranen New York, da Connecticut a karshen watan Oktoba na bara.

Lokacin da aka gano XBB.1.5 a Amurka, kasar Sin tana dinga aiwatar da tsauraran matakan rigakafin kamuwa da cutar. Ko dai nau’in cutar na BA.5 ce a halin yanzu ta zama ruwan dare a Sin, ko kuma sabon nau'in XBB.1.5 ne aka gano, an dai samu kwayar cuta ne bayan Amurka, da sauran kasashen duniya.

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin na kokarin daidaita manufofin rigakafi, da shawo kan annobar, tare da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Annobar tana kara lafawa, kuma tattalin arzikin kasar yana farfadowa.

Tun daga ranar 8 ga watan nan na Janairu, kasar Sin za ta daina daukar matakan rigakafin cututtuka masu yaduwa ga wadanda za su shigo kasar Sin daga ketare, da kayayyakin da za a shigar da su kasar Sin, galibin kasashen duniya sun gamsu da wannan matakin da kasar Sin za ta dauka.

Sabanin haka, Amurka a ko da yaushe tana siyasantar da rigakafin cutar tare da mayar da matakan abun zargi. Baya ga mayar da ita matsayin "kasa ce wadda take matsayin farko a duk duniya ta gaza yaki da cutar”, sakamakon haka, ita ce ta haddasa yaduwar cutar a fadin duniya, har ma ta hana sauran sassan duniya ci gaban yaki da annobar. (Safiyah Ma)