logo

HAUSA

Sin ta kara tabbatar da wadatuwar kayayyaki da makamashi da daidaiton farashi

2023-01-05 17:22:18 CMG Hausa

Taron majalisar gudanarwar kasar Sin wanda firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta a ranar Talata, ya yanke shawarar cewa, kasar Sin za ta kara daukar matakai don tabbatar da ganin an samar da isassun kayayyakin marasufi da makamashi da daidaiton farashi, don biyan bukatun jama'a na yau da kullum da tallata kayayyakin kamfanoni,

Taron ya kuma yi nuni da cewa, a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki, da kara karfinta na tabbatar da samar da isasshen abinci da makamashi, lamarin da ya samar da ginshiki mai karfi wajen daidaita ayyukan tattalin arziki da biyan bukatun jama'a.(Ibrahim)