logo

HAUSA

Yadda gwamnatin Sin ke dora muhimmancin kan jama’a

2023-01-04 09:56:41 CMG Hausa

A ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2022 da muka yi ban kwana da ita ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekarar 2023, inda ya tabo muhimman abubuwan da suka faru a shekarar da ta kare gami da manyan nasarorin da kasar ta cimma.

Ya bayyana cewa, duk da cewa duniya na fama da matsalar karancin abinci, amma kasar Sin ta samu girbin hatsi mai armashi a cikin shekaru 19 a jere, lamarin da ya ba da tabbaci ga al’ummar Sinawa wajen samun isasshen abinci, da kokarin kasar na ci gaba da inganta sakamakon da muka samu wajen yaki da fatara, da kokarin farfado da yankunan karkara daga dukkan fannoni. Sa’an nan mun warware matsalolin da kamfanoni suka fuskanta ta hanyar rage kudin harajin da suke biya, baya ga taimaka wa jama’a wajen warware matsalolinsu.

Bayan barkewar annobar cutar COVID-19, ko da yaushe gwamnati na tsayawa tsayin daka kan fiffita muradu da rayukan jama’a a kan komai, daukar matakan rigakafin cutar bisa ilmin kimiyya yadda ya kamata, da kuma kyautata matakan bisa sabon halin da ake ciki, hakan ya sa kasar ta yi nasarar kare rayukan jama’a da lafiyarsu gwargwadon iko. Yanzu kasar Sin ta shiga wani sabon yanayin rigakafin cutar COVID-19, kowa na ci gaba da kokarinsa, kuma tabbas za mu samu nasara ba da jimawa ba. Don haka, Jama’a, a kara kokari, idan aka dage tare da hada kai, to za mu samu nasara.

Dukkan wadannan nasarori na da nasaba ne da namijin kokarin al’ummar Sinawa da ba za a iya lissafa su ba suka cimma. Kuma wannan shi ne karfin kasar Sin. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)