logo

HAUSA

Shugaban Mozambique ya sha alwashin tallafawa tsaron kasa da kasa yayin da kasar sa ta zama mamba a kwamitin tsaron MDD

2023-01-04 11:14:23 CMG Hausa

Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, ya sha alwashin wanzar da tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, yayin da kasar sa ta samu gurbin zama mamba da ba ta dindindin ba a kwamitin tsaron MDD.

A jiya Talata ne Mozambique ta fara wa’adin shekaru 2, a kwamitin na tsaro, kuma a cikin sakon sa ga al’ummar Mozambique, wanda ya wallafa a shafin facebook, shugaba Nyusi ya ce gwamnatin sa na mayar da hankali ga kare muradun Mozambique, da nahiyar Afirka, da sauran kasashe masu tasowa, da ma duniya baki daya, musamman a fannin wanzar da tsaro da zaman lafiya, ta yadda hakan zai haifar da daidaito, da ci gaba mai dorewa ga daukacin bil adama.  (Saminu Alhassan)