logo

HAUSA

Albishir Ga ’Yan Kasuwar Ketare Dake Kasar Sin

2023-01-04 22:21:31 CMG HAUSA

DAGA Ibrahim Yaya

Tun lokacin da kasar Sin ta sanar da inganta matakanta na yaki da annobar COVID-19, kanana da manyan harkoki na kasuwanci ke kara bunkasa a sassa daban-daban na fadin kasar. Tituna sun kara cika da ababan hawa, wuraren shakatawa da na motsa jiki ma ba a bar su a baya ba.

Ana haka ne kuma, sai hukumomi suka sanar da kaddamar da sauyi a dokar gudanar da rijistar hada-hadar cinikayyar kamfanonin ketare dake cikin kasar, duk da nufin kara bunkasa harkokin kasuwanci a kasar.

A karkashin wannan sauyi, hukumomin da abun ya shafa, sun dakatar da neman takardun rajistar kasuwancin waje, daga kamfanonin dake hada hadar shige da ficen hajoji, da takardun shaidar rajistar fasaha ta kwangilolin shige da fice, da shaidar kayyade hajoji, da takardun shaidar gudanar da kasuwanci na gwamnati, da ma wasu sauran takardu masu nasaba da hakan. Matakin dake kara tabbatar da alkawarin kasar na kara zurfafa bude kofa.

Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin a nata bangare, ta ce wannan sauyi na da matukar muhimmanci ga masu gudanar da harkokin kasuwancin waje dake kasar Sin. Kaza lika sabon salo ne da gwamnatin Sin ta bullo da shi domin bunkasa cinikayya, da sakarwa kasuwa mara.

Masu fashin baki na cewa, matakin zai taimaka wajen kyautata damar gudanar da kasuwanci a saukake, da ingiza damar bunkasa cinikayyar kamfanonin waje, da bunkasa cinikayya mai nagarta, da kara bude kofa bisa matsayin koli.

Wani rahoton bincike ya nuna cewa, a cikin ’yan shekarun nan, manyan kamfanonin kera kayayyaki na kasar Sin, sun samu ci gaba matuka, inda kasuwar ta kara samun darajar da ma fadada tasirinta a kasuwannin ketare.

A halin da ake yanzu, yawan kamfanonin kera kayayyaki masu hannun jari dake rukuni na A ko A-share a Turance, ya kai 2,121, wanda ya karu da kashi 69.7 bisa dari daga 1,250 a karshen shekarar 2017. Yayin da darajar manyan kamfanonin kera kayayyaki a kasuwa da aka zayyana, sun karu sosai daga shekarar 2017 zuwa ta 2021. Wadannan kamfanoni sun samu kudin shiga da yawansu ya kai yuan tiriliyan 11.79 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.69, a cikin kudaden shiga na ayyukan da suka gudana a shekarar 2021, idan aka kwatanta da yuan tiriliyan 7.47 a shekarar 2017. Wannan na kara nuna cewa, manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje na kara amsa sunanta. (Ibrahim Yaya)